Daga Ibrahim Muhammad Kano
Jigo a jam’iyyar ADC a Jihar Kano, Hon. Magaji Ya’u Indabawa, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa nasarar gudanar da taron dattawan Kano masu katin zaɓe, waɗanda ke goyon bayan takarar Alhaji Atiku Abubakar.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Kwamared Idris Ibrahim Unguwar Gini, ɗaya daga cikin masu fafutukar ganin Atiku Abubakar ya samu nasara a zaɓen 2027.
Hon. Indabawa ya ce al’ummar Kano da ’yan Najeriya baki ɗaya su zaɓi Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, a zaɓen 2027 domin kuɓutar da ƙasar daga matsalolin da take ciki.
Ya ce abin da ake magana a kai yanzu ya wuce siyasa kawai, domin lokaci ya yi da ya kamata ’yan Najeriya su yi abin da zai taimaka wajen ceto ƙasar daga matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.
Musamman ya yi kira ga ’yan Arewa da su fahimci cewa idan aka sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, matsalolin da ake fuskanta za su iya ci gaba da ƙaruwa.
Ya ƙara da cewa rashin zaman lafiya zai ci gaba da ƙaruwa, yana mai cewa babu wata muhimmiyar ajandar gwamnatin tarayya da ta sanya Arewa a sahun gaba, ko kuma ta samar wa yankin adalci yadda ya kamata.
“Saboda haka, duk abin da za a yi, ya kamata talaka ranar zaɓe ya zaɓi Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar,” in ji shi.
Hon. Indabawa ya ce bai kamata wani ya yi tunanin cewa za a kawo wani ɗan siyasa a Kano a tilasta wa jama’a su zaɓe shi ba, musamman ganin irin yadda ya ce aka raina tare da cin mutuncin al’ummar yankin.
Ya ce a halin yanzu, Arewacin Najeriya na buƙatar shugaba da ya fahimci matsalolin yankin kuma zai iya magance su, yana mai bayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan siyasar da ba ya nuna ƙabilanci.
“Abin da yake so shi ne ya haɗa kan Najeriya, a yi wa kowa adalci, a tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa, sannan a farfaɗo da noma,” in ji shi.
Magaji Ya’u Indabawa ya kuma yi magana kan tsadar man fetur, inda ya ce farashin fetur ya tashi matuƙa tun bayan zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu.
“Mutumin nan Tinubu ya zo mulki ana sayar da fetur N180. Yanzu ko a mafarki idan aka ce zai mayar da fetur N1,350, sai a ce ƙarya ne. Wannan abin ya kamata mu sani. Dole mu fito mu ƙalubalanci wannan gwamnati,” in ji shi.
Ya yi kira ga magoya bayan Atiku da su tsaya tsayin daka wajen kare ƙuri’unsu a lokacin zaɓe.
“Mu tsaya a ko’ina mu kare zaɓenmu. Babu wanda zai iya canza mana abin da muka zaɓa,” in ji shi.






