Daga Haidar Aliyu
An taya Shaikh Dr. Sajjad Abubakar Nasir Sajjad murnar samun matsayin “Ambassador of Peace” bayan kammala wasu kwasa-kwasai kan Inter-Religious Dialogue, Conflict Transformation and Mediation cikin nasara.
An gudanar da kwasa-kwasan ne a Zariya da Birnin Tarayya Abuja, inda NILE University da Veritas University suka ba shi takardar shaidar kammala karatun.

Haka kuma, an karrama shi da lambar yabo daga COFP Foundation bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin al’umma masu addinai daban-daban.

Masu taya Dakta Sajjad murnar sun bayyana wannan nasara a matsayin wata babbar ci gaba da za ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarinsa wajen yaɗa zaman lafiya, sasanci da fahimtar juna a cikin al’umma.

Sun kuma yi addu’ar Allah Ya kara masa ɗaukaka da samun nasarori tare da ba shi ikon sauke nauyin wannan matsayi yadda ya kamata.








