Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban Hukumar jin daɗin Alhazzai na ƙasa, Farfesa Saleh Abdallah Pakistan, ya yi kira ga waɗanda suka koyi sana’o’i na dogaro da kai ƙarƙashin Matasan Arewa Family su yi ƙoƙarin gina kansu da shi don taimakawa kansu da iyaye da ‘yan’uwa da sauran al’umma.
Ya yi karan ne a yayin yaye matasa 300 da Matasan Arewa Family suka koyawa sana’o’i a ɓangarori daban-daban da aka gudanar a makarantar Gwagwarwa wanda mai bai wa shugaban hukumar Alhazan na ƙasa shawara a kan siyasa, Alhaji Albani Mai Zoɓo ya wakilta.
Ya ce akwai fom da aka bai wa shugaban hukumar Alhazai na ƙasa na matasa da za a koyawa sana’o’i ya turo matasa 21 domin su koya dama ya yi fice a wannan ɓangaren Malami ne na addini mai bayar da tarbiyya, kullum yana jan hankalin maza da mata su dogara da kai duka abin da kake ya zama kana da sana’a..
Alhaji Albani Mai Zoɓo ya ce yawanci ɗalibai da aka koyawa sana’o’i ‘yan mata ne da suka koyi harkar kwalliya na zamani, kuma suka gama, don haka ne Farfesa Saleh Abdallah Pakistan ya bai wa mutum 21 tallafi na kayan yin kwalliya da za su dogara da kansu bayan yaye su da aka yi kamar yadda sauran shugabanni na APC kowa da ɓangaren tallafi da ya ɗauka zai yi wasu na girki wasu na masu sola.
Ya ce sun ba da tallafin jari na yin kwalliya ga ‘yan mata da suka koya ne ƙarƙashin Gidauniyar Abdallah Saleh Pakistan shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, kuma shaidar karramawa da matasan Arewa Family suka bayar ya karɓa madadinsa yana daga cikin waɗanda suke karɓa da ba su san iya yawan su ba, domin k
Ƙololuwa ma dai sun karɓi na Ƙasa Mai Tsarki saboda ingancin Malamin da ya jagoranci gudanar da aikin Hajji cikin nasara a bana da aka yi wa Alhazai kyautatawar da ba a yi musu irin ta ba a baya.
Ya ce mahajjata sun ji daɗin karramawar ta gida da matasa suka yi kuma ƙarin kwarjini ne. Suna godiya.
Alhaji Albani Mai Zoɓo ya yi fatan samun yawaitar irin waɗannan matasa masu ɗaukar ragamar koyar da sana’o’i kamar yadda Mubarak yake a ƙarƙashin Matasan Arewa Family don taimaka wa al’umma, kowa akwai ɓangaren da zai iya yi kamar shi Farfeasa Malami ne na addini yana ba da tarbiyya ta ɓangaren addini yara da manya su san Allah da yadda za su bauta masa kowa da fanni da ya ɗauka a cikin al’umma.
Alhaji Albani Mai Zoɓo ya yi kira ga ɗalibai da suka amfana su kula da ba su kaɗai ba ne suka sami wannan dama ta koyon sana’ar, amma wasu zuwa ɗaya, biyu suka yi suka daina zuwa sai su da suka dage suka tsaya suka koya tsawon wata uku, kuma aka tallafa musu da jari.
Ya ci gaba da cewa, “Dama Farfesa Imam Saleh Abdallah Pakistan a matsayinsa na Malami ya fi so ka zo da sana’a da za ka dogara da kai a tallafa maka. Don haka mata da suka sami horo aka ba su tallafi su riƙi sana’a har gidan aurensu.”
Shi ma wanda ya yi wa jam’iyyar APC takarar majalisar jiha a ƙaramar hukumar Nasarawa a zaɓen 2023, Hon. Aminu Umar Faruk da aka fi sani da DBD a yayin taron yana daga wanda aka karrama, ya kuma ɗauki nauyin tallafa wa ɗalibai 10 daga cikin waɗanda aka yaye.
Ya ce lokacin da ake koyar da sana’o’i suna zuwa gani da ido, ga shi har sun gama an yaye su, wasu sun koyi kwalliya, wasu sa fitilar sola, wasu girki-girke .
Ya yi kira ga waɗanda aka horar su jajirce su zama mutane masu dogara da kai domin lokacin da iyayensu suka turo su koyon waɗannan sana’o’i ba kuɗi suke ba su na abin hawa da suke zuwa ba, amma sun dage sun yi. “Don haka yaran sun burge mu sosai, sun tsaya sun koya. Mafi yawansu wannan alama ce ta za su tsaya su riƙe sana’ar da aka koya musu .
Hon. Aminu Umar Faruk DBD, wanda kuma shi ne shugaban Gidauniyar DBD, ya ce shi ma ya kawo yara kusan 28 da aka koyawa sana’o’i a ɓangaren kwalliya da sa fitilar sola da wanda suka koyi girke-girke.”
Shi ma jagoran Matasan Arewa Family, Muhammad Mubarak da ya assasa koyawa matasan sana’o’i ya gode wa mutane da suka halarci taron yaye ɗaliban da irin tallafi da suka yi wa waɗanda aka yaye da kayan da za su iya kama sana’a su dogara da kawunansu musamman Farfesa Imam Saleh Abdallah Pakistan shugaban hukumar Alhazai ta Ƙasa.
Muhammad Mubarak ya yi kira ga mutane masu hali da masu riƙe da muƙamai da ƙungiyoyi su riƙa sa hannu domin taimakawa irin wannan tsari na horar da matasa a kan sana’a, domin hakan zai taimaka wajen rage zaman rashin aikin yi ga matasa, ya kuma kange su daga faɗawa aikata yin abin da bai dace ba.
Cikin waɗanda aka karrama a yayin taron yaye ɗaliban da aka koyawa sana’o’i akwai tsohon shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, tsohon Kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar Kano Hon. Lamin Sani Kawaji, wanda ya sami wakilciin mataimakinsa na musamman.







