Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Zagayowar Watan Mauludeen Nabiyyi (SAW)

Daga Ibrahim Muhammad

Tsohon Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Hon. Ibrahim Namadi Dala, ya bayyana mutuƙar farin cikinsa da shigowar wata mai albarka na haihuwar Annabi Muhammad (SAW) Rabi’ul Awwal.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi a kan su yi ƙoƙarin nuna soyayya ga Annabi (SAW) da yin koyi kyakkyawan ayyukansa da hakan zai sa a samu dacewa da rahamar Allah Maɗaukakin Sarki, wanda shi ne ya umurce da nuna soyayya ga Manzon Allah a kowane yanayi.

Hon. Ibrahim Namadi Dala ya yi wa al’ummar Musulmi na jihar Kano da na ƙaramar hukumarsu ta Dala fatan cigaba da samun alkhairin da ke cikin wannan wata na Mauludeen Nabiy mai albarka.

Sannan ya taya Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso murnar shigowar wannan wata da yin fatan duk abin da suka sanya a gaba na alkhari Allah ya tabbatar da shi.

Hon. Ibrahim Namadi Dala ya yi kira ga al’ummar Musulmi da cewa a duk lokacin da aka zauna wajen majalisan Maulidi a sanya ƙasar nan da jihar Kano a addu’a da nufin Allah ya kawar da dukkan damuwa, ya tabbatar da yalwar arziƙi da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo