Muna Son Atiku, Za Mu Zaɓe Shi Domin Muna Sa Ran Zai Taimaki ’Yan Najeriya -Hussaini Ɗan Birni Jibrin

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon Mataimaki na Musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Hon. Hussaini Ɗan Birni Jibrin, wanda aka fi sani da Hussaini Paki, ya bayyana dalilin da ya sa ya ajiye muƙaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar APC.

Hon. Paki ya bayyana haka ne yayin taron dattawan masu goyon bayan Atiku Abubakar na Jihar Kano, wanda Kwamared Idris Ibrahim Unguwar Gini ya shirya.

Ya yaba da ƙoƙari da jajircewar Kwamared Unguwar Gini wajen shirya taron, yana mai cewa ƙungiyar da yake jagoranta ta san halin da manoma da ’yan kasuwa ke ciki a ƙasar nan.

“Ni a matsayina na Shugaban Ƙungiyar Groundnut Farmers Youths Network, wadda take da tsari a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan, mun san irin cin mutuncin da aka yi wa manoma da wulakancin da aka yi wa ’yan kasuwa. Mun kuma san irin ƙabilancin da ake nuna mana.

“Wannan ne ya sa muka yanke shawara cewa, idan dai muna da kyakkyawan tunani, musamman mu ’yan Arewa, ba sai an ce maka kada ka zaɓi Tinubu ba,” in ji shi.

Hon. Hussaini ya ce shi da kansa ya gana da Sanata Barau Jibrin, inda ya miƙa masa takardar ajiye aikinsa.

“Na ce masa ba zan ƙara yin Tinubu ba, domin na san halin da muke ciki na masifa. Ba zan iya nuna maka aiki guda ɗaya da aka yi wa Arewa ba, sai matsalar rashin tsaro, tsadar rayuwa, talauci, ƙunci da ƙabilanci.

“Duk wani abu mai amfani a Arewa an ɗauke an kai Kudu. An bar mu da gaba da ’yan’uwanmu Fulani. Mu Hausa da Fulani mun zama ɗaya. Za ka ga mutum a Arewa mahaifinsa idan ba Bafulatani ba ne, mahaifiyarsa Bafulatani ce,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a Kudu ba a fuskantar irin waɗannan abubuwa, yana mai kira ga al’ummar Arewa da su duba halin da suke ciki kafin zaɓe.

“Saboda haka, a wannan yanayi mu duba kanmu. Ba Waziri za mu taimaka wa ba. Kada mu yaudari kanmu. Masifar da muke ciki yanzu, wallahi bilahil azim, ba sai an ce ka fita ka tallata Waziri ya samu nasara ba,” in ji shi.

Hon. Hussaini Dan Birni Jibrin ya ce zaɓe ne ke sa a kafa gwamnati, yayin da addu’a da gwagwarmaya suke taimakawa wajen sauya gwamnati.

“Harkar cin zaɓe ba wani abu ba ne. Ka je ka tsaya ka bi layi ka dangwala ƙuri’arka. Ka kyautata mu’amala da jama’a, da ’yan’uwa da maƙwabta. A je a yi zaɓe a ƙasa a tsare.

“Tabbatar da wanda za ka yi hulɗa da shi yana da katin zaɓe, domin akwai ɗan siyasa da ba ya zaɓe, amma ya iya tayar da hayaniya,” in ji shi.

A ƙarshe, Hon. Hussaini Dan Birni Jibrin ya yi kira ga al’umma da su tashi tsaye wajen tabbatar da an zaɓi Atiku Abubakar a matsayin Shugaban Ƙasa.

“Muna son Waziri, za mu zaɓe shi domin muna kyautata masa zato, shi ne zai taimaki ’yan Najeriya, ya kuma ceci ’yan Arewa da ake cutarwa. Shi ne ya fi ƙarfin ya ci zaɓe, ko a kwace masa,” in ji Hon. Hussaini Dan Birni Jibrin.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum