Daga Ibrahim Muhammad
An yi kira ga ma’aurata da cewa kowa ya yi haƙuri domin zaman mata da miji a harkar rayuwa sai an haɗa da haƙuri.
Manajan Daraktan kamfanin Getawa, Alhaji Ibrahim Muhammad ne ya bayyana hakan a wajen walimar auren ‘ya’yansa da aka gudanar a ranar Juma’a.
Ya yi nuni da cewa irin harka ta rayuwa da kowanne tsakanin Amarya da Ango da suka saba da ita a gidansu ba ita zai gani a rayuwarsu ta aure ba.
Ya ce su a matsayinsu na iyaye suna jan hankalin waɗanda aka aurar da cewa za su ga canjin rayuwa a inda za su je, haka shi ma miji wanda ya auro idan ta zo gidansa rayuwa da ta saba a gida ba ita za ta tarar ba.
Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya ce ma’auratan kowa ya yi haƙuri, yadda suke son junansu har aka kai ga aure in suka yi haƙuri babu wanda zai ji kansu, kuma Allah zai ba su zaman lafiya da zuriya mai albarka.
Ya ce suna yi wa Allah godiya da ya nuna masa wannnan taron ɗaurin aure da aka yi shi lafiya aka gama lafiya, ‘yan’uwa da abokan arziƙi da suka zo taya su murna ya yi fatan Allah ya saka wa kowa da alkhairi .
Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya yi addu’ar Allah ya zaunar da ma’auratan lafiya ya kare su dukkan fitina ya sanya alkhairi da albarka a auren.







