Daga Ibrahim Muhammad
Tsohon ɗan Majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano, Hon. Alhasan Uba Idris na shirin gudanar da taron dukkan magoya bayan jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Dala.
Taron zai mai da hankali ne a kan nuna goyon bayan tafiyar Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Jibrin Maliya mataimakin shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa.
Za a gudanar da taron ne gobe Asabar a ɗakin taro na nazarin ɗamakwaraɗiyya Mambayaya Gwammaja.
Hon. Alhasan Uba Idris dai shi ne Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin ‘yan Majalisun Jihar Kano na jam’iyyar APC.







