GWAMNAN LAWAL YA JADDADA ƘUDURINSA NA BAIWA ƁANGAREN SHARI’A ‘YANCIN KANSU DON SAMAR DA ADALCI A ZAMFARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen ba da fifiko ga tsare-tsare da ke inganta tabbatar da adalci a kan lokaci da kuma kare ’yancin ɓangaren shari’a.Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da ma’aikatan kotuna a babbar kotun shari’a ta Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a harabar babbar kotun da ke Gusau.A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, taron ya samar da wata dama ga jami’an shari’a da masu ruwa da tsaki domin tantance ayyukan da bangaren shari’a ke yi, da gano ƙalubale, da kuma kafa sabbin manufofi.A jawabinsa na bufe taron, Gwamna Lawal ya amince da jajircewa da jagoranci na ƙwarai na Babbar Alƙalin Alƙalan Jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu, OFR, FNJI, da ɗaukacin bangaren shari’a bisa jajircewarsu na sauke nauyin da aka ɗora musu.Ya ce, “jajircewarta wajen tabbatar da adalci yana ƙara ƙwarin gwiwa da kuma ƙara wa bangaren shari’a aminci a matsayin wata cibiya mai muhimmanci a tsarin dimokuraɗiyya. Wannan gwamnati ta tsayu tsayin daka wajen tallafa wa bangaren shari’a a dukkan ayyukanta.”Gwamnatina za ta ci gaba da ba da fifiko ga shirye-shiryen da za su inganta samar da adalci a kan lokaci da kuma kare ‘yancin wannan bangare na gwamnati.”Gwamna Lawal ya bayyana cewa, taron ƙara wa juna sanin na da matuƙar muhimmanci. “Zai inganta fasaha da kuma ilimantar da mahalarta domin su kasance cikin shiri sosai don yin hidima da biyan buƙatun jama’a. Jama’ar mu na kallon ku a matsayin matita ga talakan ƙasa wajen ganin ya samu adalci tare da kare haƙƙinsa. Dole ne jami’an shari’a da ma’aikatan su kasance cikin shiri sosai don cimma waɗannan manufofi, musamman a waɗannan lokutan da ake fuskantar ƙalubale.“Babbar Alƙalin Alƙalai, alƙalan babbar kotun jihar Zamfara, manyan mahalarta taron, abin farin ciki ne ganin irin matakan da hukumar shari’a ke ɗauka wajen tsare-tsaren ma’aikatan Majistare da sauran ma’aikatan shari’q domin tabbatar da adalci.Gwamnan ya kuma buƙaci bangaren shari’a da su yi taka-tsan-tsan a kan wasu ’yan tsirarun da ɗabi’unsu za su iya gurgunta mutuncin wannan hukuma. “Ganowa tare da magance rashin ɗa’a a bangaren wani nauyi ne da ke buƙatar himma, mutunci, da sadaukarwa.”

Related Posts

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum