A Litinin ɗin nan ne, gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Sanata Uba Sani, CON, ta kira taron masu ruwa da tsaki don nazarin nasarori da matsalolin da aka samu a zaɓen cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar.
Taron ya samu halartar mataimakiyar gwamna Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Rt. Hon. Yusuf Ɗahiru Liman, da manyan jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki na jam’iyya, shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli, da kuma magoya bayan jam’iyyar APC.
A wani ɓangare na taron, an tattauna kan ƙarfafa ƙoƙarin masu riƙe da madafun iko don kyautata wa jama’ar da suka zaɓe su da kuma himma wajen isar da kudurorin cigaba na gwamnatin jihar Kaduna.






