Daga Ibrahim Muhammad
An yi kira ga masu riƙe da madafun iko ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da mawadata a tsakanin al’umma a kan su cigaba da taimaka wa mata da marayu da gina cigaban matasa kamar yadda a koyaushe Hon. TJ. Ƙaura Goje yake yi.
Hajiya A’isha Isah Abubakar Gama CEO ta Masruk Universal Concept, shugabar mata ta gidan Hon. Tijjani Abubakar da aka fi sani da T.J. Ƙaura Goje Liason Officer na Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a jihar Legas ta yi kiran a wajen yaye ɗalibai da Matasan Arewa Family ta koyawa sana’o’i a ƙaramar hukumar Nasarawa.
Ta ce ta yi mutuƙar jin daɗin taron, tare da yabawa masu ba da horon, shi ya sa ma ta zo ta ɗan ba su gudunmuwa don ƙarfafa musu gwiwa a kan ƙoƙarin da suke na koyawa matasa sana’o’i domin su zama masu dogaro da kai da amfanar al’umma.
Hajiya A’isha Isah Abubakar ta ce jagoran gidansu na siyasa, Hon. T.J. Ƙaura Goje kamar katafila ne sarkin aiki da yake taimakawa matasa, mata da marayu da sauran mabuƙata koyaushe, shi ya sa a kullum yake tare da jama’a.
Ta ƙara da cewa, Hon. Tijjani Abubakar Ƙaura Goje shugaba ne da yake koyi da jagoransu na Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen kyautatawa da bunƙasa cigaban al’umma.
Hajiya A’isha ta ce, babu inda Hon. T.J. Ƙaura Goje ba ya taɓawa domin aiki da ba nasa ba ma yana yi, kullum a taimakon mabuƙata, mata da marayu yake da bayar da gudunmawar aure da na cigaban ilimi.






