Gwamnatin Kano Ta Shirya Taron Bunƙasa Ƙananan Masana’antu Da NASSI Da Stanbic IBTC

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Zuba Jari, Ciniki, Kasuwanci da Masana’antu ta jihar Kano ta bayyana cewa taron yini ɗaya da aka gudanar domin bunkasa ƙananan da matsakaitan masana’antu a jihar ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Kano.

Ta bayyana hakan ne a yayin wani taro da Gwamnatin Kano, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Masu Ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta Ƙasa (NASSI), suka shirya, wanda Bankin Stanbic IBTC ya ɗauki nauyin gudanarwa a Kano.

Ta ce jigon taron shi ne samar da hanyoyin magance matsalolin da ke fuskantar ƙananan da matsakaitan masana’antu, tare da gina yanayi mai kyau na gasa da bunƙasa kasuwanci a jihar Kano.

A cewarta, taron ya zo a daidai lokacin da yake da muhimmanci, domin manufarsa ta yi daidai da ɗaya daga cikin abubuwan da Gwamnatin Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta sanya a gaba, na samar da yanayin da zai sauƙaƙa harkokin kasuwanci, ta yadda kamfanoni za su iya farawa, su dore, su bunƙasa, su ƙirƙiri sabbin abubuwa, su samar da ayyukan yi tare da yin gogayya cikin nasara da sauran ƙasashen duniya.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar NASSI na ƙasa, reshen jihar Kano, Alhaji Aminu Ibrahim Kurawa, Ɗan Masanin Ma’ajin Watari, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma da su ci gaba da bai wa ƙungiyar goyon baya domin ta ci gaba da samar musu da damarmakin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana gamsuwarsa da taron, inda ya ce jami’an hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jihar Kano sun halarta, an yi tambayoyi tare da warware wasu daga cikin matsalolin da ke fuskantar masu ƙananan masana’antu. Ya ce an kuma gabatar da shawarwari da matakai da ake sa ran za su taimaka wajen ci gaban masana’antun nan ba da jimawa ba.

Alhaji Aminu Kurawa ya nuna jin daɗinsa kan yadda Bankin Stanbic IBTC ya shiga cikin shirin domin tallafa wa ƙananan masana’antu, yana mai cewa bankin ya yi alkawarin taimaka musu wajen samar da wutar lantarki da kuma jari cikin sauƙi, waɗanda ya bayyana a matsayin wasu daga cikin manyan matsalolin da ke fuskantar masu masana’antu.

Ya ƙara da cewa sun kuma sanar da Gwamnatin Kano wasu daga cikin matsalolin haraji da suke fuskanta, inda ya ce Gwamnatin ta nuna aniyar ɗaukar matakai domin ganin an magance matsalolin.

Shi ma Shugaban Ƙungiyar Masu Ƙananan Masana’antu ta Dakata, Alhaji Zulkiflu Alhassan Umar, ya bayyana jin daɗinsa da taron da NASSI tare da Bankin Stanbic IBTC suka shirya.

Ya ce taron ya kasance mai matuƙar amfani ga masu ƙananan masana’antu na Dakata, yana mai cewa yankin na daga cikin wuraren da ake samun ɗimbin ƙananan masana’antu a ƙasar nan.

Ya ce taron ya haɗa hukumomi daban-daban, ciki har da NAFDAC, SON da KEDCO, inda aka wayar da kan masu masana’antu kan hanyoyin gudanar da harkokinsu yadda ya kamata da kuma bin ƙa’idojin hukumomin da abin ya shafa.

Zulkiflu ya ce masu masana’antu a Dakata suna samun wutar lantarki, amma matsalar ita ce tsadar ta, don haka ya yi kira da a duba hanyoyin sassauta musu farashin wutar.

Ya kuma ce bayan matsalar gobarar da ta faru a yankin, suna buƙatar tallafin jari domin farfaɗo da sana’o’insu, yana mai kira ga Bankin Stanbic IBTC da ya taimaka musu wajen samun jari.

A ƙarshe, ya yabawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa tallafin naira miliyan 10 da ya bai wa mutanen da gobarar ta shafa.

  • Related Posts

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Africa Academy, wadda ke gudanar da karatu ta yanar gizo ƙarƙashin Africa TV3, ta gudanar da bikin yaye dalibai 3,500 da suka kammala karatun Diploma…

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sanya Wazirin Magani na jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar,…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano