Al’ummar Kano Su Yi Amfani Da Damar Mallakar Hannun Jari A Kamfani Ɗangote — Junaid Zakari

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Kasuwar Singa, Barista Junaid Muhammad Zakari, ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su yi amfani da damar da aka samar ta sayen hannun jarin Matatar Man Ɗangote.

Barista Junaid, wanda kuma shi ne Shugaban Dandalin Shugabannin Kasuwannin Jihar Kano, ya bayyana ƙaddamar da sayar da hannun jarin da aka gudanar a Kano a matsayin wani mataki na kusantar da wannan dama ga jama’a.

Ya ce mutum na iya mallakar hannun jari a matatar da Naira 5,250 kacal, yana mai cewa wannan dama ce da aka samar domin bai wa ’yan Najeriya damar kasancewa cikin masu mallakar hannun jarin matatar.

Ya bayyana cewa an wayar da kan jama’a kan muhimmancin sayen hannun jarin, musamman ta fuskar tattalin arziƙi da bunƙasa dukiya, tare da bayyana cewa an kuma tabbatar da ingancinsa ta fuskar addini.

Barista Junaid ya ce, duk da cewa wasu na ganin farashin hannun jarin ya yi ƙasa, akwai fatan waɗanda suka yi amfani da damar, daga Naira 5,250 zuwa sama, za su samu damar bunƙasa dukiyarsu nan gaba.

Ya ƙara da cewa an sauƙaƙa tsarin sayen hannun jarin, inda mutum zai iya gudanar da aikin ta bankuna tare da amfani da lambar BVN.

Barista Junaid Muhammad Zakari ya kuma yi kira ga ’yan kasuwa da su taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi da ke aiki tare da su wajen samun hannun jarin, domin su ma su amfana da damar da aka samar.

  • Related Posts

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Africa Academy, wadda ke gudanar da karatu ta yanar gizo ƙarƙashin Africa TV3, ta gudanar da bikin yaye dalibai 3,500 da suka kammala karatun Diploma…

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sanya Wazirin Magani na jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar,…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano