Daga Ibrahim Muhammad
Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha ta bayyana shirinta na saka ƙafar wando ɗaya da duk wani gidan wasa da ɗakunan taron da aka samu da yin rashin ɗa’a a yayin gudanar da bikin Babbar Sallah.
Hukumar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai kewaya gidajen wasannin tare da ɗakunan taro a ranakun Babbar Sallah ƙarƙashin kulawar Alh. Lawan Hamisu Ɗan Hassan Daraktan da ke lura da sashin finafinai na Hukumar.
Kwamitin, wanda aikinsa shi ne saka ido a kan dukkannin gidajen wasannin da dakunan taro a jihar Kano, haɗi da masu kiɗan DJ zai tabbatar ba a bai wa masu shigar banza ko shaye-shaye damar shiga gidajen wasannin ba ko ɗakin taro.
Haka kuma, Hukumar ta hana hada maza da mata a guri ɗaya a yayin bikin na Babbar Sallar.
Abba El-mustapha ya ce kwamitin zai rinƙa aiki ne a dare da rana ta cikin sirri, tare da bayyane tun a rana 1 ga Zulhijja aka fara, har zuwa lokacin da za a kammala bikin Sallar domin cimma nasarar aikin da aka sa a gaba.
Abba El-mustapha na ƙara yin gargaɗi da kakkausar murya ga masu gidajen wasanni da ɗakunan taro, tare da masu sana’ar DJ da su bi dokokin Hukumar sau da ƙafa domin guje wa fushin doka.
A ƙarshe ya yi kira da iyaye da su cigaba da kula da tarbiyyar ‘ya’yansu, tare da addu’ar Allah ya sa a yi bikin na Sallah lafiya a gama lafiya.








