IPAC Kano Ta Nemi Haɗin Kan Jam’iyyu Domin Yin Zaɓe Mai Inganci A 2027

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Kungiyar Zauren Shawarwarin Jam’iyyu ta Kasa, Reshen Jihar Kano, wato IPAC, ta gudanar da taro na musamman da shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar.

Taron na da nufin neman haɗin kai domin tabbatar da gudanar da zaɓe sahihi, karɓaɓɓe, kuma ba tare da tashin hankali ba a zaɓen 2027 mai zuwa.

Shugaban IPAC na Jihar Kano, Hon. Isah Nuhu Isa Ɗanfulani, ya bayyana cewa sun kira jam’iyyun ne domin tattaunawa kan wannan manufa. Ya ce jam’iyyun sun nuna amincewa da za su haɗa kai da yin aiki tare domin cimma burin.

“Jam’iyyun sun tabbatar da cewa za a samu haɗin kai yadda za a gudanar da dukkan zaɓe cikin lumana da kwanciyar hankali,” inji Hon. Ɗanfulani.

Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummar jihar, musamman waɗanda ba su da katin zaɓe, da su yi gaggawar yin rajista. Ya ce, “Katin zaɓe ne kaɗai zai ba ‘yan ƙasa damar zaɓar waɗanda suke so a zaɓen 2027”.

Taron ya samu halartar wakilan jam’iyyu daban-daban sama da 12, tare da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar jihar Kano.

  • Related Posts

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo