Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Hajiya Dakta Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, ta ce manufarta ita ce ci gaba da tallafa wa matasa masu karatu da masu sana’o’i, tare da ƙarfafa musu gwiwa domin su dogara da kansu.
Ta bayyana haka ne yayin da take jawabi ga wasu matasa, inda ta ce tana bai wa matasa dama su shiga ƙungiyar masu yaɗa ayyukanta a kafafen sada zumunta, amma da sharadin cewa suna da abin yi.
Hajiya Balaraba ta ce duk wanda zai ce shi ɗan kafafen sada zumunta ne na Balaraba, amma ba shi da aiki ko kuma ba ya zuwa makaranta, to ba zai ci gaba da kasancewa cikin ƙungiyar ba.
“Abin da na fi so shi ne matasa su nemi sana’a. Gara in san kana da sana’a sannan ina taimaka maka. Burina shi ne kowa ya kasance yana aiki, ko yana karatu, ko kuma yana da wata hanyar dogaro da kai. Siyasa sai da sana’a, domin dukkanmu muna da abin da muke yi,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa tarbiyyar da suka samu daga iyayensu ita ce ta mutunta al’umma da kuma taimaka musu ba tare da gajiyawa ba.
“Yau za mu yi taimako, gobe ma za mu yi, idan an sake nema washegari ma za mu yi. Haka muka taso muka ga iyayenmu suna yi. Muna mutunta al’umma kuma ba za mu daina ba. Muna kuma fatan ‘ya’yanmu su ci gaba da wannan kyakkyawar ɗabi’a,” in ji ta.
Hajiya Dakta Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta kuma ce duk wanda zai yi mu’amala da su dole ne ya kasance mai kyakkyawar hulɗa da al’umma, mai mutunta mutane, mai son abin da Allah Ya umarta, kuma mai ƙin abin da Ya hana. “Shi ne ginshiƙin rayuwarmu gaba ɗaya,” in ji ta.







