Daga Ibrahim Muhammad Kano
Kwamishinan Ma’aikatar Wuta da Makamashi ta Jihar Kano, Dakta Gaddafi Sani Shehu, ya yaba wa cibiyar tuntuɓa da gudanar da harkokin ilimi “Chiranci Educational Management Consultancy Services” karkashin jagorancin Malam Aminu Ya’u, bisa ƙoƙarinta na zaburar da ɗaliban makarantu kan yin rubutu da bincike.
Wannan yabo ya fito ne ta bakin Hon. Abubakar Ibrahim Nasir Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Harkokin Makamashi, wanda ya wakilci Kwamishinan a wajen taron raba kyaututtuka ga ɗaliban da suka yi fice a gasar rubutu da cibiyar ta shirya.
Hon. Abubakar ya ce ba abin mamaki ba ne karramawar da aka yi wa Dakta Gaddafi, saboda mutum ne da aka sani da kishin ilimi da hidima, musamman a Ƙaramar Hukumar Gwale da faɗin jihar Kano baki ɗaya.
Ya kara da cewa; “Dama Kwamishinan ya saba taimakon ɗalibai a harkar karatu. Duk lokacin da aka buƙaci goyon bayansa a harkar ilimi, yana bayar da gudunmawa.”
Hon. Abubakar ya kuma jinjinawa cibiyar Chiranci bisa wannan shiri, inda ya ce abin a yaba ne da kuma buƙatar gwamnati ta ɗauki nauyin tallafawa irin waɗannan ƙungiyoyi domin su ƙara haɓaka ilimi a jihar.
A nasa jawabin kuma, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi Manajan Darakta na Hukumar Kogunan Haɗejia da Jama’are, ya jaddada muhimmancin rubutu a matsayin na ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.
Ya ce: “Turawa da sauran ƙasashe masu ci gaba sun ba rubutu muhimmanci, shi ya sa suka samu ci gaba. Abin da cibiyar Chiranci ke yi na koyar da yara tun suna ƙanana muhimmancin rubutu abin yabo ne.”
Alhaji Rabi’u Sulaiman ya yi kira ga matasa da su daina ɓata lokaci wajen amfani da kafafen sada zumunta mara amfani. “A Nijeriya muna amfani da social media wajen shirita da ɓata lokaci. Amma a wasu ƙasashe kamar China, ba ka da damar buɗe wani shafi sai dai don aikata abin da zai kawo ci gaba, ba shiririta ba,” in ji shi.
Mahalarta taron sun yaba da irin ƙoƙarin da cibiyar Chiranci Educational Management Consultancy ke yi wajen gina makomar ɗalibai ta hanyar haɓaka basirar rubutu da bincike.








