Allah (SWT) ya bai wa Wazirin Katsina na biyar, Farfesa Sani Abubakar Lugga, MFR damar wallafawa da samar da littatafai masu yawan gaske a matsayin wani ɓangare na yi wa al’umma hidima da nufin bunƙasawa da ciyar da ilimi gaba.
A cikin wannan watan Zulhijjah 1446 Hijira kaɗai, ya wallafa littattafai masu mujalladai 25, a ciki littattafai 119 da ya samar. Kuma ya ɗora wasu 46 a shafinsa na intanet: www.luggaweb.com. Mutane za su iya amfana da kuma mallakarsu kyauta, tare da yin taƙaitaccen bayani a kan wasu 25.
A yanzu akwai jimillar littattafai 71 a wannan gidan na yanar gizo: www.luggaweb.com
Nan gaba kaɗan za bayyana hanyoyin samun kwafin duk waɗannan littattafan.








