Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban Kwalejin Islamiyya da Ilimin Zamani ta Zam Zam, Alhaji Sabitu Ahmad Usman Kazaure, ya yaba wa makarantar bisa irin gudunmawar da take bayarwa wajen gina yara kan kyakkyawar tarbiyya, tare da ba su ingantaccen ilimi.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana bayan bikin yaye ɗaliban da makarantar ta gudanar, inda ya ce bikin abin alfahari ne ga iyaye, musamman ganin irin hazaka da ɗalibai suka nuna.
A cewarsa, abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda ɗaliban firamare suka gabatar da ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire, ciki har da ƙera jirgin ƙasa, matatar ruwa da kuma nuna yadda ake tace ruwa.
Ya ce a baya ba a cika samun irin waɗannan ayyuka a matakin firamare ba, domin galibi ana ganinsu ne a manyan makarantu.
“Mun gode wa Allah da Ya ba mu makaranta irin wannan da ke fitar da yara masu ilimi tare da tarbiyya. Wannan babban abin alfahari ne ga iyaye,” in ji Alhaji Sabitu.
Ya ƙara da cewa abin da ya ja hankalinsa har ya zaɓi kai ‘ya’yansa makarantar shi ne yadda take haɗa ilimin addini da na zamani, tare da mai da hankali sosai kan tarbiyyar ɗalibai.
Ya yi kira ga iyaye da su ba ilimin ‘ya’yansu muhimmanci, yana mai cewa a wannan zamani da ake fama da ruɗani, ilimi da tarbiyya su ne manyan makaman da za su kare al’umma.
Haka kuma, ya ce yawancin matsalolin tsaro da ake fuskanta a yau na da alaƙa da rashin tarbiyya da ilimi tun daga ƙuruciya. Saboda haka ya buƙaci iyaye su riƙa kula da abokan hulɗar ‘ya’yansu, tare da tabbatar da cewa suna cin gajiyar lokutan hutu ta hanyar karatu da sauran abubuwan da za su amfane su.
Alhaji Sabitu ya kuma yaba wa masu gudanar da Kwalejin Zam Zam da sauran makarantu masu zaman kansu bisa ƙoƙarin da suke yi wajen inganta ilimi a ƙasa.
Sai dai ya buƙaci gwamnati ta ƙara zuba jari a makarantun gwamnati domin bai wa kowane yaro damar samun ingantaccen ilimi, yana mai cewa ba kowane iyaye ne ke da ikon biyan kuɗin makarantun masu zaman kansu ba.
“Ita gwamnati ce uwar kowa, don haka ya kamata ta tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi mai inganci,” in ji shi.








