Kwamishinan lafiya Na Jihar Kano Ya Yaba Wa Shugabanni Ƙananan Hukumomin Ajingi, Gaya, Wudil Kan Nasarar Rigakafin Shan-Inna

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya nuna gamsuwa da yadda shirin rigakafin shan-inna yake tafiya a ƙananan hukumomin Ajingi, Gaya da Wudil.

Kwamishinan ya nuna gamsuwar ne a ranar Lahadin da ta gabata jim kaɗan bayan kammala duba aikin a wasu sassa na ƙananan hukumomin.

Ya ce ya ji daɗi sosai da yadda ya ga jama’a sun karɓi shirin hannu bibiyu, wanda shi ne jigon samun nasarar shirin a yankin. Yana mai yaba wa ma’aikatan lafiya na ƙananan hukumomin wajen tabbatar da yi wa dukkanin yaran da suka cancanta rigakafin.

Kwamishinan ya jinjina wa shugabancin ƙananan hukumomin saboda kyakkyawan aikin da suka yi na bin tsare-tsare da aiki tare kamar yadda aka tsara tun daga matakin jiha, da kuma yadda suke halartar tarukan nazarin yadda aikin ya gudana a kowace rana.

Ya ce, “Abin farin ciki ne ganin yadda shugaban ƙaramar hukumar Gaya yake zuwa ko’ina a yankin domin tabbatar da an yi wa yaran da suka cancanta rigakafin ba tare da tsallake yaro ko ɗaya ba.

“Ƙari kan haka, shugaban ƙaramar hukumar yakan bayar da tallafin magunguna da kayayyakin aiki a asibitoci don inganta harkokin lafiya a yankin.

“Bugu da ƙari, an ga mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Wudil yana kai kawo a lungu da saƙo na yankin domin tabbatar da shirin ya cimma nasara a yankin,” inji shi.

Dakta Labaran, wanda Daraktan Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa na Ma’aikatar Lafiya, Dakta Ibrahim Aliyu Gano ya wakilta, ya yaba wa jajircewar hakiman yankunan game da rawar da suke takawa don samun nasarar shirin a matsayinsu na iyayen ƙasa, da kuma yadda suke halartar tarukan duba yadda aikin ya gudana a kowace rana, inda a wasu lokutan suke tura wakilai idan ba za su samu damar zuwa ba.

Ya buƙaci iyaye da su ci gaba da kai yaransu da suka cancanta cibiyoyin yin rigakafi da aka ware ko kuma su bar ma’aikatan da ke bi gida-gida suna yi wa yaran rigakafin domin a daƙile ɓurɓushin cutar shan-inna da aka fara samu a wasu sassa na jihar nan, don haka akwai buƙatar haɗa hannu wajen tukarar matsalar.

Daga nan sai kwamishinan ya buƙaci jami’ai masu wayar da kan mutane kan kiwon lafiya a yankunan da su ƙara ƙaimi wajen ilimantar da al’umma su fahimci baƙatar da ake da ita ta su bai wa ma’aikata masu bi gida-gida cikakken haɗin kai domin kuɓutar da yaransu daga wannan cuta mai illa.

Dakta Labaran ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na yadda ya mayar da fannin lafiya ɗaya daga cikin manyan ƙudurorin da gwamnatinsa ta bai wa fifiko wanda tuni kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum