Daga Ibrahim Muhammad
Kakakin Gwamnan jihar Kano, Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yana bakin ƙoƙarinsa wajen taimakon ‘yan jam’iyyar.
“Ni dai a sani na ban taɓa ganin Gwamnan da ke taimakon ‘yan jam’iyyarsa ciki har da ‘yan gwagwarmaya ba kamar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf”.
Gwamna ya raba kujerun Makka da na raba Umrah, ya raba babura, motoci da gidaje, kuma yana ba da jari a gwamnatance da kuma ta aljihunsa kai tsaye.
Wannan na kunshe ne cikin wani rubutu da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce, “Tun da aka ƙirƙiri jihar Kano babu Gwamnan da ya ba da tallafi ga masu marasa lafiya cikin ‘yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki da sauran al’ummar gari kamar Gwamna Abba Gida Gida.
Sai dai ya ce hannun Gwamna ba zai kai kan kowa ba saboda yawan mutane, kuma akwai haƙƙi a kan su da ya ɗorawa nauyi na mukamai, ba su da wani uzuri idan ba su rage masa aiki ba wajen tallafawa na ƙasa da su ko kuma makusantansu a wannan harkar.
Ya ce da yawanmu muna ƙoƙari wajen rage nauyin, amma wasu gajen haƙuri ne da su, wasu kuma Wallahi ba ma mu san sun ba da gudunmawa ba, saboda mutanen da yawa.
Amma ba laifi ba ne idan an ci gaba da haskawa jami’an gwamnati waɗanda suka sha walaha a harkar kuma suke da buƙatar taimako.
“Wallahi ko irin su SSAs ɗin nan da kuke gani irin su Salisu Yahaya Hotoro da Muhammad Sani Isah Romi da su Abubakar Muhammad Inuwa da ma Salisu Ƙosawa suna samun abin da za su taikamaki ‘yan’uwansu ‘yan gwagwarmaya,” in ji Sanusi Bature.
Saboda haka babu wani uzuri ga waɗanda suka ƙi taimakon ‘yan jam’iyya musamman waɗanda aka yi gwagwarmayar yaƙin neman zaɓe a 2019 da 2023 da su.
Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ƙara da cewa, “Ni dai kam, kada Allah ya ba ni abin da ba zan iya taimakawa wani da shi ba, ko mene ne na gidan duniyar nan.







