Kwamitin Zagayan gari na Maulidi Yaba Majinyata 70 talfi a Asibitin Funtua

Daga Hussaini Yero
Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (saw) na Funtuwa da kewaye ya kai ziyara ga Majinyata da ke kwance a Asibitin Dandutse da Karamin Asibitin Funtua ya kuma ba Majinyata 70 tallafi kudin dan sayan magani ga kowane su .
Shugaban Kwamitin Busiri Muhammad Kin, ya bayyana cewa, wannan Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (saw) na yankin Funtuwa,na daga cikin ayyukan Kwamitin shine tallafawa marasa lafiya da kuma ziyarar Gidan Gyara hali ,inda a bana Kwamitin ya ceto mutane takwas daga gida Gyara hali na garin Funtuwa.kuma ayau gamu cikin wadannan Asibitici na Dandutse da Karamin Asibitin Funtua,munba kowane majinyaci naira dubu biyu kuma Majinyata 70 suka amfana da wannan tallafi ayau daga Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (saw) na yankin Funtua .
 Anasu Jawabin Kalifan Tijaniya Ali Sa’idu Alti da Malam Aminu Inuwa Zakiru ,sun bayyana cewa,jinya ibadace da Allah ya ke jarabtar bayan sa a koda yaushe hatta Annawan Allah suna gamuwa da jarabawa ta rashin lafiya dan haka zaman jinya da kukeyi ibada ne a wajan Allah.ziyara gareki shima ibada ce wanda Manzan Allah ya umarce mu da muyi dan haka muka kawo maku wannan ziyara da kuma dan tallafi na sayan magani,albarkaci murnar haihuwar Manzan Allah (saw).
Kalifa Ali Sa’idu Alti ya jinjinawa Dahiru Barau Mangal kan ciyarwa da yakeyi a Asibitin ga Majinyata akan haka ne, Kalifa yayi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da ciyarwa irin ta Dahiru Barau Mangal da taimakon marasa lafiya masu kwance a Asitici.
Kuma Kalifan Tijaniya ya kuma yabawa Malam Asibiti akan yadda suke kula da marasa lafiya da kuma kula da tsaftar Asibitin.
Ansasu jawabin Shugabanin masu kula da Asibitocin,Dr Abdulhadi da Dr Dan Gaye,sun mika godiyar su ga Kwamitin zagayan aka  tallafawa marasa lafiya dan yanzu haka akwai majinyantan da basu da kudin sayan magani amma zuwanku ya taimaka masu .akan haka muke godiya a gareku da wannan aiki na alhairi da kukeyi Allah ya taimaki wannan Kwamitin zagayan gari kamar yadda kuka taimaki Majinyatan mu Amin.
Anasa jawabin Shugabanin Karamar Hukumar Funtua,Malam Lawal Sani da ya samu wakilcin,Kamsila Mai kula da lafiya Hon, Mansur Dan Bello ya bayyana godiyar sa ga wannan Kwamitin da fatan sauran Kwamitoci da kungiyiyi zasu koyi da ku wajan taimakon marasa lafiya da kuma wadanda ke zaune a gidan Gyara hali na ceto masu Kannan laifuka.kamar yadda kukeyi.

Related Posts

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo