Daga Ibrahim Muhammad, Kano.
Sabon Shugaban Riƙo na Ƙungiyar Kasuwar Sayar da Waya ta Bata Global GSM, Nura Baffa da akafi sani da Nura Kansila, ya ce harkar waya na daga cikin sana’o’in da ke samar da aikin yi ga dubban matasa a Jihar Kano.
Da yake jawabi bayan rantsar da shi da Ma’aikatar Kasuwanci ta Jihar Kano ta yi a kwanakin baya, Nura Baffa ya ce kasuwar na ba da gudummawa sosai wajen dogaro da kai.
Ya bayyana cewa harkar waya “sanai’a ce mai sirri da albarka”. “Za ka iya ganin tebur guda ɗaya, amma ka tarar da murum biyar suna cin abinci a kai. Wani zai ajiye wayarsa guda ɗaya ya tafi, ya barwa mai tebur don a sayar masa, ya samu wani abu,” in ji shi.
Shugaban ya ce da ƙaramin jari na N10,000 ko N5,000 matashi zai iya fara sana’ar waya. “Muddin ka tsaya da gaskiya da amana, ba za ka rasa na abinci da buƙatun rayuwa ba gwargwadon hali.Sannan akwai waɗanda suka ƙware a gyaran waya, akwai masu sayar da kayayyakinta.”
Nura Baffa ya ce shugabancinsa zai fito da sabbin tsare-tsare na taimaka wa matasa wajen samun sana’o’in dogaro da kai da kuma kawar da hankulansu daga shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da shiga daba.
“Da zarar matasa sun tashi da sana’a, hakan zai katange su daga aikata abubuwan da ba su dace ba,” ya ce.
Ya kuma jaddada cewa zai ba da kulawa ta musamman ga harkar tsaro, domin tsaro na daga cikin manyan ƙalubalen da kasuwannin waya ke fuskanta. “Za mu yi aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a kasuwar.”
Shugaban kasuwar, wanda aka fi sani da Nura Baffa Kansila, ya yabawa ‘yan kasuwa bisa goyon bayan da suka bayar wajen samar da shugabancin. Ya kuma yi kira gare su da su ba da haɗin kai domin ganin ci gaba da bunƙasar kasuwar Bata Global GSM.






