Makarantar Tanwirul Azhar Li Tahafizil Kur’ani Ta Yi Taron Saukar Ƙur’ani Da Maulidin Annabi (S)

Daga Ibrahim Muhammad

An gudanar da taron saukar karatun Ƙur’ani Karo na biyar na makarantar Tanwilur Azhar Li Tahafizil Ƙur’an a ranar Lahadi.

Taron ya sami halartar iyayen ɗalibai maza da mata da iyayen ƙasa da manyan gwanayen Alƙur’ani.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a taron saukar wanda ya assasa makarantar Malam Muhammadul Hadi da ake wa laƙabi da Malam Bala ya ce, an assasa makarantar ne kusan shekaru 13 da manufar sunanta na “Kore duk wani abu na rashin sani a ƙwaƙwalwa a cusa masa Alƙur’ani da Tarbiyya”, sun fara ne da ɗalibai daga rumfarsa ta gida da ɗalibai ‘ya’yansa biyar da malamai biyu, amma karatun da suke yi ya janyo makarantar sai da ta zama tana da ɗalibai 32 a cikin gidansa. Daga nan ya sama mata wajen zama ta rushe gidansa ya mayar muhallin makarantar na dindindin, yanzu kuma tana da ɗalibai sama da 500 da malamai 42.

Ya yi nuni da cewa dama can iyaye da kakanninsu na karantar da Alƙur’ani a Allo a tsarin Tsangaya har yanzu suna nan kan Tsangayar mahaifinsa, sai suka ga cancantar faɗaɗa karatun ya tafi da zamani yadda ake buƙata.

Ya ce babban nasara da kafa makarantar ta samu shi ne kore rashin tarbiyya, a duk inda reshen makarantar take da tabbatar da tarbiyya dan haka ma za ka samu yaron da mahaifinsa suka gaza ko wani dalili ya sa sun ɗauke shi daga makarantar, amma yana da shauƙin zuwa makarantar, ko da ba a turo su ba, suna cuɗeɗeniya da ɗaliban makarantar saboda sha’awarsu da tarbiyya da kyakkyawan mu’amala da ake da shi

Malam Bala ya ce tunda suna da Tsangaya ta Allo sun fahimci ƙalubale daban-daban da suka saba da su, amma da suka shigo wannan tsari sai suka samu sauƙin ƙalubalen, saboda kowane Uba sai ya yi wa ɗansa rijista ya yarda da manufa da tsarukan makaranta.

Ya yaba da irin gudunmawa da iyaye da maƙwabta ke ba su, kuma koyaushe suna ba su haƙuri a kan duk abin da zai je ya zo domin zama da ɗan wani sai haƙuri ko naka ne ma haƙuri kake da shi, suna yi musu juriya, kuma suna neman shawarwari daga gare su kowane yanayi ana fahimtar juna.

Malam Muhammadul Hadi ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu da hukumomi duk wata ƙa’ida da Hukumar Ilimi ta ƙaramar hukumar Gwale a kanta suke tafiya sau da ƙafa suna ba su haɗin kai, kuma sun sami tallafi na malamai daga gwamnati ana bai wa malamai da makarantar ta ɗauka horo na sanin makama.

Malam Balarabe ya yaba da irin gudunmawa da malaman makarantar ke bayarwa da tare da jan hankalinsu da cewa su ƙara duba rayuwar al’umma a wannan lokacin da ake ciki duk wanda ya yi wa ɗan wani gudunmawa na alkhari, Allah zai yi wa nasa ko yana raye ko baya nan, kuma su iyaye su zama masu haƙuri da hangen nesa in ka bar ɗanka bai tafi makaranta ba a cikin wace ɗabi’a zai kasance su waye za su zama abokansa, don haka su ɗora su kan nema ilimi.

Saukar karatun dai na wannan karon na ɗalibai guda 65 ne daga ciki maza 33 da kuma ɗalibai mata guda 32.

An raba takardu na shaidar yabo ga malamai da wasu daga cikin al’umma da suke bayar da gudunmawa ga cigaban ilimi da tarbiyya.

Bayan kammala bukin saukar makarantar ta ɗora da gudanar da Maulidin Annabi da ta shirya.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength