Mun Kafa Kwalejin Kimiyar Lafiya da Fasaha Ta ARYAN Don Cike Giɓin Ma’aikatan Lafiya – MLS Shamsu Garba

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An kafa Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta ARYAN da ke Birnin Kudu, jihar Jigawa, ne domin horas da ɗalibai da inganta harkar kula da lafiyar al’umma, la’akari da ƙarancin irin waɗannan cibiyoyin ilimi a faɗin Nijeriya, ba jihar Jigawa kaɗai ba.

Shugaban Kwalejin (Provost), MLS Shamsu Garba, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa, inda ya ce an kafa Kwalejin ne bayan bin dukkan matakan da doka ta tanada, tare da cika ƙa’idojin da hukumomin gwamnati suka shimfiɗa kafin a ba su sahalewar fara karatu.

Ya ce, tun bayan fara koyarwa, al’umma sun nuna gamsuwa da tsarin ilimi da horo da Kwalejin ke bayarwa, lamarin da ya sa iyaye ke yawaita kawo ’ya’yansu domin neman ilimi a makarantar.

A cewarsa, a halin yanzu Kwalejin na karɓar ɗalibai a zangon karatu na biyu, inda ake koyar da fannoni daban-daban na kimiyyar kula da lafiya, duk da cewa adadin ɗaliban bai yi yawa ba, amma harkokin koyarwa na tafiya yadda ya dace.

MLS Shamsu Garba ya ƙara da cewa Kwalejin na da yarjejeniyar fahimta (MoU) da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa, bayan da jami’an ma’aikatar suka duba tsarin koyarwa da horon aiki, suka kuma amince da shi. Wannan haɗin gwiwa ya bai wa ɗaliban Kwalejin damar yin aikin koyon sana’a (SIWES/Practical) a manyan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a faɗin jihar, ciki har da Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kudu.

Ya alaƙanta nasarorin da Kwalejin ke samu cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da tsari, jajircewa da haɗin kan ma’aikata da shugabanci, inda ya ce an gina komai tun daga tushe bisa tsari nagari.

A sakamakon haka, Kwalejin ke karɓar ɗalibai daga jihohi daban-daban da suka haɗa da Kano, Adamawa, Kaduna da sauran sassan ƙasar nan.

A matsayinsa na ƙwararre a fannin kiwon lafiya mai dogon ƙwarewa, MLS Shamsu Garba ya jaddada cewa dole ne duk wani abu da ya shafi lafiyar al’umma ya kasance bisa ƙa’ida da tsari.

Ya ce nasarar Kwalejin ta samo asali ne daga kasancewar masu kafa ta ƙwararru a fannin lafiya, abin da ya ƙara gamsar da iyaye da al’umma baki ɗaya, tare da ganin amfanin ilimin da ake bai wa ’ya’yansu.

Ya ce ko da su ba su rayu ba nan gaba, wannan cibiyar ilimi za ta cigaba da amfanar al’umma, domin an kafa ta ne da nufin bayar da gudunmawa wajen bunƙasa lafiyar jama’a, wanda shi ne babban burinsu tun farko.

Shugaban Kwalejin ya kuma bayyana cewa a tsarin tafiyar da Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta ARYAN, ana sauƙaƙa sharuddan shiga matuƙar ɗalibi na da ingantattun shaidun karatu da doka ta tanada. Wani lokaci ma, a cewarsa, Kwalejin kan bai wa ɗalibai damar fara karatu ko da ba su da cikakken hali na biyan kuɗin makaranta, inda daga baya za su biya idan sun samu dama. Ya jaddada cewa har yanzu masu tafiyar da makarantar ba su fara cin ribarta ba, domin manufarsu ita ce taimakon al’umma.

A ƙarshe, MLS Shamsu Garba ya yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta ƙara tallafawa irin waɗannan makarantu na kimiyyar lafiya, domin ƙarfafa ayyukansu da kuma tafiya da buƙatun tsarin kiwon lafiya na zamani.

Haka kuma, ya yaba wa iyaye bisa haɗin kai da suke bai wa makarantar, tare da bayyana cewa a duk ƙarshen zangon karatu, Kwalejin kan zaƙulo haziƙan ɗalibai domin ƙarfafa musu gwiwa ta hanyar kyaututtuka, abin da ke ƙara zaburar da ɗalibai wajen jajircewa a karatu.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum