Ibrahim Al Amin “Little” A ADC: Shirinsa Na Ceto Jihar Kano A 2027

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Alhaji Ibrahim Al Amin, wanda aka fi sani da “Little”, fitaccen ɗan siyasa ne, kuma ɗan kasuwa daga Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.

An san shi da karamci, tausayi da kuma kishin taimakon jama’a, musamman matasa da marasa ƙarfi. Tun kafin shiga siyasa, ya kasance kusa da al’umma ta hanyar tallafi da ayyukan jin ƙai.

Alhaji Ibrahim Al Amin “Little” ya fara harkokin siyasa ne a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP, wadda a lokacin ta kasance babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya. Shigarsa jam’iyyar ya ƙara mata ƙarfi a Kano, inda ya zagaya kananan hukumomi 44 na jihar wajen gina tubalin jam’iyyar har ya kai ga zama shugabanta a Kano.

A shekarar 2003 ya nemi tikitin takarar Gwamnan Kano a ƙarƙashin ANPP, inda ya kayar da Malam Ibrahim Shekarau a zaɓen fid da gwani. Daga baya ya fice daga ANPP zuwa PRP, kafin daga bisani ya shiga APC a shekarar 2015 domin mara wa Muhammadu Buhari baya.

Sai dai bayan ya nuna rashin gamsuwa da salon mulkin Buhari da kuma tafiyar APC, ya sauya sheƙa zuwa PDP.

A zaɓen 2023, ya mara wa Alhaji Atiku Abubakar baya tare da gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓe a Kano domin samun nasarar jam’iyyar.

A shekarar 2025 ya sake ficewa daga PDP sakamakon rikice-rikicen cikin gida da abin da ya bayyana a matsayin rashin dimokiraɗiyya a jam’iyyar. Daga nan ne ya koma jam’iyyar ADC, wadda ta zama mafakar haɗin gwiwar ‘yan adawa masu neman sauyi a Nijeriya.

Yayin da siyasar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, Alhaji Ibrahim Al Amin “Little” ya bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin ADC, tare da bayyana cewa lokaci ya yi da za a kawo sabon salo na shugabanci a jihar.

Masu goyon bayansa na ganin yana da hangen nesa da zai iya kawo sauyi a fannoni da dama da suka haɗa da kasuwanci, ilimi, lafiya da bunƙasa rayuwar matasa.

Daga cikin manufofinsa akwai samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin rage matsalar rashin wuta, tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha, gyaran makarantu daga matakin Firamare zuwa Jami’a, da kuma inganta ayyukan asibitoci.

A matsayinsa na ɗan kasuwa, ya bayyana aniyarsa ta jawo masu zuba jari, tallafa wa ƙananan masana’antu da samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci domin bunƙasa tattalin arzikin Kano.

Alhaji Ibrahim Al Amin “Little” ya sha bayyana cewa matasa da talakawa su ne ginshiƙin siyasa, ba masu kuɗi da manyan mutane kaɗai ba. A cewarsa, hakan ne ya sa yake ci gaba da kasancewa tare da jama’a, yana sauraron matsalolinsu tare da ƙoƙarin tallafa musu.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum