NNPP Da APC Sun Yi Nasara A Zaɓukan Cike Gurbi Da Aka Yi A Kano

Daga Ibrahim Muhammad

Hukumar zaɓe mai zamanta ta ƙasa, INEC ta bayyana Ali Lawan Alhassan a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar jiha na ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono da ƙuri’u 16,198, yayin da na APC ya samu ƙuri’u 5,347.

Baturen zaɓen, Farfesa Hassan Adamu Shitu ne ya sanar da sakamakon da misalin ƙarfe 12:36 ba safe.

Haka zalika, INEC ta sanar Garba Yau Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙananan hukumomin Ghari da Tsanyawa.

Baturen zaɓen yankin, Farfesa Muhammad Waziri, ne ya sanar da sakamakon zaɓen da ƙarfe 6:10 na safiyar wannan Lahadi.

Farfesa Waziri ya ce jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 31,472, yayin da NNPP ta sami ƙuri’u 27,931.

Don haka ya ce Garba Ya’u Gwarmai, na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen cike gurbin na mazaɓar Ghari da Tsanyawa a majalisar dokokin jihar Kano, da aka gudanar ranar Asabar.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum