Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana ɗan Majalisar Tarayyar mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano, Injiniya Sagir Ƙoƙi da cewa mutum ne da yake tallafawa bunƙasa cigaban mata da matasa.
Hajiya Mariya Ali Zage shugaban matan Kwankwasiyya ta Saudiyya, mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Birni shawara a kan kasuwanci da hannun jari, ta bayyana hakan, ta ce yana kula da tallafa wa mata da matasa yana sayawa masu aure kayan ɗaki da kuɗi, haka idan an yi haihuwa yana tallafawa masu jego ga babura da motoci da yake bayarwa da ba da kayan abinci ko ita ya ba ta buhunan shinkafa da babu adadi ta raba wa mata gida-gida.
Hajiya Mariya Ali Zage ta ce wannan ita tasa mata kullum suke farin ciki da wakilcinsa suke masa murna da fatan ya gama ya ƙara ya yi ta wakilcin don kwalliya ta biya kuɗin sabulu a zaɓen da aka yi wa Sagir Ƙoƙi.
Ta ce haka a ƙaramar hukumar Birni ‘yan Kwankwasiyya kansu a haɗe yake tsakanin ɗan Majalisar Tarayyar da shugaban ƙaramar hukuma, Hon. Salim Hashim suna ƙoƙarin hidimtawa mutane ba tare da nuna bambanci ba.
Hajiya Mariya Ali Zage ta ce a 2027 da yardar Allah nasara tasu ce, domin aiki shi ne jama’a ke gani lungu da saƙo ba inda aikin ɗan Majalisa da shugaban ƙaramar hukumar Birni da na Gwamnan Kano bai shiga ba, domin duk koyi suke da Jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso
Ita ma Hajiya Khadija Sale da aka fi sani da Baby Municipal SSA, Sanitation Enviroment ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ta bayyana kyakkyawan wakilci da taimaka wa al’umma da ɗan Majalisar Tarayyar na ƙaramar hukumar Birni Sagir Ƙoƙi yake shi ya sa kullum yake tare da jama’a maza da mata suke tururuwar zuwa duk sha’aninsa.
Ta ce al’ummar jihar Kano su cigaba da bai wa gwamnatin jihar Kano goyon baya domin gwamnatice a buɗe duk inda Gwamna Injiniya Abba Kabir ya je mutane na tare da shi haka su jami’ansa idan an gan su kamar shi aka gani.
Hajiya Khadijah Baby Municipal ta ce, ko yanzu irin ayyuka da gwamnatinsu ta Kwakwasiyya take a jihar Kano a 2027 ba su da haufi ko wani jin ɗar-ɗar gwamnati Abba “Go Again”, Injiniya Sagir Ƙoƙi shi ma haka da yardar Allah za su yi nasara.








