Daga Ibrahim Muhammad Kano
’Yan kasuwar Titin Galadima, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman, sun gudanar da taron karrama tsohon OC na ’Yan Sandan Kasuwar, DSP Sa’idu Ɗahiru, bisa ritayar da ya yi bayan shafe shekaru 35 yana aikin ’yan sanda.
Taron karramawar, wanda ya gudana cikin nishaɗi, ya samu halartar manyan ’yan kasuwa da shugabannin kasuwar. Da yake zantawa da ’yan jarida a wajen taron, Shugaban Kamfanin Mai na Aimal, Alhaji Isma’ila Abubakar Labbo, ya ce karramawar da aka yi wa DSP Sa’idu ba ta da alaƙa da aiki kawai, illa saboda yadda suka ɗauke shi a matsayin ɗan’uwa.
Ya ce: “Yadda ya zauna da mutane lafiya da kuma gudummawar da ya bayar wajen samar da tsaro na tsawon shekaru 20 da ya yi tare da mu a Kasuwar Galadima, ya nuna cewa ya cancanci wannan karamci.”
Ya ƙara da cewa DSP Sa’idu abin koyi ne ga sauran jami’an tsaro. “Allah ya saka masa da alheri. Muna fatan matakin rayuwar da ya shiga bayan ritaya ya zama matakin arziki a gare shi,” in ji shi.
Alhaji Isma’ila Labbo ya bayyana cewa saboda soyayya da jin daɗin zama da suka yi da DSP Sa’idu, sun koya masa harkokin kasuwanci tare da ba shi shago a kasuwar domin ya ci gaba da mu’amala da su.
A nasa jawabin na godiya, DSP Sa’idu Ɗahiru mai ritaya ya bayyana farin cikinsa da jin daɗin karramawar da ’yan kasuwar suka yi masa. Ya ce ya shiga aikin ’yan sanda ne a watan Satumba na shekarar 1991, kuma cikin yardar Allah ya yi ritaya a watan Satumba na shekarar 2026, bayan shafe shekaru 35 yana hidima.
“Na gode wa Allah da na zauna da mutane lafiya har na kammala aikina lafiya. Wannan aiki ne da duk abin da ya taso, za a ce a nemi ɗan sanda. Ina fatan Allah ya ba sauran abokan aikina damar kammala aikinsu lafiya,” in ji shi.
DSP Sa’idu ya ce a lokacin da yake OC a Kasuwar Galadima, sun yi aiki tare da ’yan kasuwar bisa bin tanadin doka da kuma haɗin kai. Ya ce yana matuƙar farin ciki da yadda ’yan kasuwar suka nuna masa harkokin kasuwanci, har suka ba shi shago, abin da ya ce zai ba shi damar ci gaba da kasancewa tare da su a kasuwar.







