Za Mu Yi Riƙo Da Gaskiya Da Amana Na Wannan Sarauta Da Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi Ya Ba Ni -Sarkin Arewa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana sarautar Sarkin Arewa da Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi, ta naɗa Alhaji Ɗahiru Sa’idu Giɗaɗo, a matsayin sarauta da aka yi bisa ƙauna, yarda da aminci.

Sarkin Arewa, Alhaji Ɗahiru Sa’idu Giɗaɗo, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai.

Ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi, bisa wannan gagarumar karamci da ya nuna masa.

Ya ce wannan naɗi alama ce ta ƙauna da yarda da aka nuna masa, yana mai addu’ar Allah Ya saka wa Sarkin Kano da alheri, Ya biya masa buƙatunsa, Ya sauƙaƙa masa duk wani abu da yake damunsa, tare da ƙara wa Mai Babban Ɗaki lafiya da kuma gafarta wa marigayi Ciroma.

Alhaji Ɗahiru Sa’idu Giɗaɗo ya yi nuni da cewa, bisa irin tarbiyyar da suka samu tun daga gida da kuma wuraren da ya yi aiki, za su ci gaba da riƙo da gaskiya, amana, tausayi ga na ƙasa, da kuma taimakon jama’a kamar yadda suka tashi suna gani ana yi a gidansu.

Ya jaddada cewa: “Za mu yi riƙo da gaskiya da amana a wannan sarauta da Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi, ya ba ni.”

Sarkin Arewan Kano ya bayyana cewa sarautarsa ta fi karkata ne ga harkokin fada, inda ake zama a gaban Sarki, yi masa rakiya da tarba, tare da wakiltarsa a wasu taruka da muhimman al’amura idan buƙatar hakan ta taso.

Haka zalika, ya bayyana cewa asalin sarautar Sarkin Arewa da aka naɗa shi a kai sarauta ce ta Hakimi a Fadar Sarkin Kano, wadda aka aro daga tsarin masarautun Haɗejia da Sakkwato, kuma tana daga cikin muhimman muƙamai da ke cikin Majalisar Sarki a waɗannan masarautu.

  • Related Posts

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Africa Academy, wadda ke gudanar da karatu ta yanar gizo ƙarƙashin Africa TV3, ta gudanar da bikin yaye dalibai 3,500 da suka kammala karatun Diploma…

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sanya Wazirin Magani na jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar,…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano