Badaƙalar Adeniyi Adeyemi: Gwamnati Ta Raina Hankalin ‘Yan Nijeriya -Farfesa Kamilu Sani Fagge

Daga Hadi Bawa

A wannan makon ne Gwamnatin Tarayya ta fito fili ta musanta zargin da ake yi cewa wasu manyan jami’anta suna da hannu a cikin badaƙalar kafa Hukumar Sanya Hannun Jari ta Ƙasa (PFIPC) ta bogi, wadda Yarima Adeniyi Adeyemi Matthew ke jagoranta.

Ana kuma zargin Adeyemi da gudanar da asusun banki guda 34, ciki har da wasu da aka buɗe da sunayen hukumomin gwamnati.

Haka kuma, ana zarginsa da gudanar da wasu ayyuka da sunan gwamnatin tarayya, ciki har da ganawa da jami’an diflomasiyyar ƙasashen waje a Otal ɗin Wells Carlton da ke Abuja ƙarƙashin tutar hukumar da halartar wasu taruka na ƙasa da ƙasa.

Duk da gwamnati ta bayyana rashin masaniya a kan ayyukan Adeyemi, amma wasu takardu da jaridar PUNCH ta samu sun nuna cewa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ya bayar da umarnin a ware wa shugaban ‘hukumar’ ofishi a hawa na biyu na Sakatariyar Gwamnatin Tarayya. Takardar, mai lamba Ref. No. SH/DG/PFIPC/RQ/107, tana ɗauke da kwanan watan 7 ga Nuwamban 2024.

A ranar 27 ga Oktoban 2025, jami’an tsaro sun taɓa kama Adeyemi tare da gurfanar da shi a gaban kotu bayan gudanar da bincike a gidansa da ofishinsa, inda aka ce an samu shaidun da ake buƙata domin hukunta shi.

A ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan wanda ake zargin, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, na cikin jerin mutane 10 da ake sa ran za su ba da shaida. Daga bisani, kotu ta ba da belin Adeyemi.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda da dama ke nuna mamakin yadda gwamnatin ke ƙoƙarin nesanta wasu jami’anta daga badaƙalar.

Da yake tsokaci kan lamarin, Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami a Tsangayar Kimiyyar Siyasa ta Jami’ar Bayero, Kano, ya ce akwai abubuwa da dama da ke nuna cewa gwamnati ba za ta iya cewa ba ta san da hukumar ba.

“Gwamnati ta ce an kafa wannan hukuma ba tare da saninta ba. Amma wannan magana ba ta yi daidai ba. Na farko, an ba hukumar ofishi a cikin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja. Ba zai yiwu a ce an kafa ofishi a irin wannan wuri ba tare da sanin gwamnati ba.

“Na biyu, an ba hukumar ma’aikata 314, kuma ana biyan su albashi. Haka kuma, kasafin kuɗin hukumar yana cikin kasafin kuɗin Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta amince da shi, sannan Shugaban Ƙasa ya sanya wa dokar hannu. Ta yaya za a ce ba a san da hakan ba?

“Bugu da ƙari, an ware wa hukumar sama da Naira biliyan ɗaya, yayin da ake kashe kusan Naira miliyan 800 wajen biyan albashin
ma’aikatanta.

“Har ma da jakadun ƙasashe daban-daban sun yi hulɗa da hukumar. Idan aka dubi waɗannan bayanai, za a fahimci cewa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na nesanta kanta da hukumar tamkar kau da hankalin jama’a ne daga babbar matsalar cin hanci da rashawa da badaƙala.”

Farfesa Fagge, wanda ya yi waɗannan kalamai yayin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Kano Live24, ya ce darakta janar na hukumar ya yi zargin cewa ya kashe kuɗaɗe masu yawa kafin ya samu damar jagorantar hukumar.

“A cewarsa, daga baya wani babban mutum ya nemi a ba shi kaso mai tsoka daga cikin kuɗaɗen da aka ware wa hukumar, kusan kashi 40 cikin 100. Daga nan ne aka samu sabani har lamarin ya rikide zuwa rikici,” in ji shi.

Ya ce bai kamata gwamnati ta yi watsi da zarge-zargen ba, sai dai ta gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya. “Hausawa na cewa idan mai faɗin magana wawa ne, bai kamata mai sauraro ya zama wawa ba. Wannan ba ƙaramin lamari ba ne. Ana maganar kuɗaɗen al’umma da kuma cin amanar ƙasa. Ya kamata a bincika lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace.

“Shi ya sa ma Femi Falana ya bayyana cewa za su garzaya kotu domin a ɗauki matakin da ya dace.

“Yau idan ka je gidajen gyaran hali, za ka tarar da mutane da aka tsare saboda satar kuɗin da bai kai Naira dubu biyar ba. Amma a nan ana maganar miliyoyin kuɗi da kuma hulɗa da ƙasashen waje, sannan a ce an bar wanda ake zargi ya tafi a haka.”

Jaridar PUNCH ta tuntuɓi Hukumar EFCC domin jin ta bakinta, sai dai kakakinta, Dele Oyewale, ya ƙi cewa komai.

Haka kuma, Yomi Odunuga na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce ba zai ce komai ba sai ya kwafin takardar da ake zargin sun ba da umarnin a ba Hukumar ofis.

  • Related Posts

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Africa Academy, wadda ke gudanar da karatu ta yanar gizo ƙarƙashin Africa TV3, ta gudanar da bikin yaye dalibai 3,500 da suka kammala karatun Diploma…

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sanya Wazirin Magani na jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar,…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano