Daga Ibrahim Muhammad
Makarantar Raudatul Jannah da ke Rangaza ta ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano, ta gudanar da walimar haddar Ƙur’ani ga ɗalibai 45 na makarantar.
Taron da aka gudanar a ranar Lahadi, ya sami halartar ɗimbin iyayen yara daga ciki da wajen ƙasar nan da shugabannin al’umma da malamai.
A yayin taron saukar mahaddatan, an gabatar da kalandar makarantar, inda mutane da dama suka bayar da gudunmawa wajen ƙaddamarwa.
Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan kammala walimar, Imam Muhammad Yakubu, Darakta na rukunin makarantun Raudatul Janna ya ce, walimar saukar ita ce ta huɗu, sun yi sauka ta farko a 2018, inds aka yaye yara takwas suka yi musaffa ta Ƙur’ani. Sannan suka sake yaye 16 a karo na biyu. Sannan a karo na uku aka yaye 21. Wannan ta huɗu cikin wannan shekara ta 2025 an yaye yara 45, Hafizai da suka yi musaffa ranar Laraba, Lahadi kuma aka yi bukin yaye su.
Ya ce nasara da suke samu ta danganta ne da yin abu da iklasi da jajircewa, domin idan za ka yi abu ka sa Allah a gaba zai ba ka nasara kamar lokacin da Imam Malik ya rubuta Muwaɗɗa Maliku ne, sai aka ce masa ai an yi Muwaɗɗa da yawa kafin shi, sai ya ce a kawo ya duba. Da aka kawo sai ya ce ‘za ku ga cewa waɗanda aka yi tsakani da Allah shi ne zai wanzu. Yanzu malamai da almajirai da yawa ba su san akwai wats Muwaɗɗa ba bayan Muwaɗɗar Maliku saboda ita ya yi da iklasi ta wanzu.’
Imam Muhammad Yakub ya ce farin cikin su shi ne na ganin yara ƙanana sun haddace Ƙur’ani, kamar yadda suka yaye wata yarinya mai Hauwa’u ‘yar shekara shida da ta haɗa hadda a shekara ɗaya. Abin mamaki kuma akwai wani yaro Al-Amin wanda ya gama haddarsa yana ɗan shekara bakwai, ire-iren waɗannan abubuwa na ban mamaki na abin arziƙi ba ne ba akasin haka ba, abin da ake yi yana ba da mamaki yana yin fice babu shakka abin su gode wa Allah ne.
Sannan ya yi kira ga iyayen yara da cewa duk haddar mutum da karatunsa yana buƙatar maraja’a da nazari ko mutumin da yake karatu a Jami’a yana yin nazari yana karatu, saboda haka idan ɗalibai suka dawo gida akwai buƙatar iyaye su sa ido a kan wannan haddar yaro bai san muhimmanci da daraja da kimar abin da ya karanta ba, amma shi mahaifi ya sani, in aka rabu da shi, babu shakka haddar za ta zube. “Don haka yara su mayar da hankali iyaye su sa ido,” ya jadadda.
Ya ce kusan kaso 80 ciki 100 na ɗalibansu da suke yayewa sune ke jan Sallar Ƙiyamul Laili a unguwanni da suka yi maƙwbataka da su. Wannan na faranta mana rai, amma ‘yan kaɗan ɗin da ba a ba su kulawa ba, sai a ga babu haddar, babu karatun. Wannan abin takaici ne,” ya ƙarƙare.
Imam Muhammad Yakub ya yi kira ga gwamnati da muƙarrabanta a kan su mayar da hankali a kan ilimin addinin Musulunci, domin idan mutum tun yana ƙarami ya sami tarbiyya, ya san haram da halak, za a sami sauƙin masu aikata laifuka, don yaro ya san abin da Allah ya hana, kuma ya ginu a haka zai yi abin da Allah yake so, amma rashin samun ilimi da tarbiyya shi yake wanzar da rashin aikin yi da rashin yin sana’a, kuma yake kawo ta’addanci a zo a yi ta wahala, kuma babu nasara, in ji shi.








