Walin Gafasa Ya Yaba Da Cigaban KASSOSA, Amma Ya Nemi A Gyara Wasu Muƙamai

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Wani mamba a ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta KASSOSA, Kwamared Awaisu Nasir Wali (Walin Gafasa), ya bayyana cewa an samu gagarumin cigaba a harkokin shugabancin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Balarabe Nuhu Jalla Ɗanbatta, sai dai ya jaddada buƙatar yin gyara a wasu muƙaman shugabanci.

Walin Gafasa ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan taron ƙarshen shekara da ƙungiyar ta gudanar a jami’ar Bayero University Kano, inda ya ce taron ya gudana yadda ya kamata, kuma ya ƙayatar matuƙa, kamar yadda aka saba gudanarwa duk shekara.

Ya ce taron ya samu armashi sosai, inda tsofaffin ɗalibai suka halarta daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ma ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa har da waɗanda ke riƙe da manyan muƙamai a fannoni daban-daban sun halarci taron, inda aka bayar da gudummawa tare da ƙarfafa zumunci a tsakanin mambobin ƙungiyar.

A cewarsa, wannan taro shi ne na ƙarshe a wannan shekara a zangon shugabancin da ake ciki, inda ya bayyana cewa, idan Allah Ya kai su, za a gudanar da taro na gaba a shekarar 2026, wanda a cikinsa ne za a sake gudanar da zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar.

Walin Gafasa ya yaba wa shugabancin yanzu ƙarƙashin jagorancin Alhaji Balarabe Nuhu Jalla Ɗanbatta bisa ƙoƙarin da suke yi wajen tafiyar da harkokin ƙungiyar, tare da ɓullo da tsare-tsare masu amfani da kuma samar da mambobi masu karsashi, kishin ƙungiyar da son cigabanta.

Sai dai ya yi nuni da cewa, duk da cewa babu wata matsala da ake alaƙantawa da mataimakin shugaban ƙungiyar, sakatare da wasu muƙamai, akwai wasu a cikin ƙunshin shugabancin da ake zargin su da aikata abubuwan da ba su dace ba, lamarin da ke jawo ƙorafe-ƙorafe daga mambobin ƙungiyar.

Ya ce irin waɗannan ɗabi’u na son rai, handama da babakere na rage kimar ƙungiyar a idanun ‘ya’yanta da ma abokan hulɗa da ke halartar tarurrukanta, lamarin da ke iya ɓata mata suna da martaba.

Walin Gafasa ya ce a matsayinsu na matasa a cikin ƙungiyar, za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an kawar da dukkan mutanen da ke ƙoƙarin raunana ƙarfin da aka gina ƙungiyar a kai.

Ya ƙara da cewa za su yi aiki tuƙuru a zaɓen da ke tafe domin sauya irin waɗannan shugabanni masu halaye da ba su dace da tafiyar da ƙungiyar ba.

A ƙarshe, Kwamared Awaisu Nasir Wali (Walin Gafasa) ya bayyana cewa duk wanda ya riƙe muƙami a zanguna daban-daban, amma bai iya magance matsalolin da suka taso ko ya ƙara gina abin da aka soma ba, ya dace a sauya shi domin kare kimar ƙungiyar.

Ya jaddada cewa da yardar Allah za a samu gyara domin ci gaban KASSOSA.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum