Iyaye da Gwamnati Su Ƙara Ba da Kulawa Ga Makarantun Alƙur’ani – Malam Mahmud TijjaniUsman Zangon Barebari

Malam Mahmud Tijjani Usman Zangon Barebari ya yi kira ga iyaye da kuma gwamnati da su riƙa ba da kulawa ta musamman ga makarantun Alƙur’ani, domin inganta tarbiyyar yara da tabbatar da makomarsu a duniya da lahira.

Malam Zangon Barebari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen walimar yaye mahaddatan Alƙur’ani da makarantar Madinatul Ahbab Daiba ta shirya a harabar Masallacin Shehu Ahmadu Tijjani, da ke Ƙofar Mata, a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa taron saukar Alƙur’ani taro ne na farin ciki da albarka, kasancewar Manzon Allah (SAW) ya umarci al’umma da su tarbiyyantar da ‘ya’yansu a kan abubuwa uku: karatun Alƙur’ani, son Manzon Allah (SAW), da kuma son Ahlul Baiti.

Malam Zangon Barebari ya ce ganin yadda yara sama da 100 suka haddace Alƙur’ani a wannan makaranta abin farin ciki ne matuƙa, inda ya ƙara da cewa malamai sun bayyana karantar da yara Alƙur’ani a matsayin abin da ke kwantar da fushin Ubangiji.

Ya ce a wannan zamani ya zama wajibi a ƙara ba da muhimmanci ga karatun Alƙur’ani tare da ƙarfafa shi.

Ya yaba da makarantar Madinatul Ahbab Daiba ƙarƙashin jagorancin Shehu Malam Dan Almajiri, inda ya ce makaranta ce mai asali da albarka, wadda ba kasafai ake samun irinta ba, face dai a yi koyi da tsarin tafiyarta.

Ya kuma bayyana taron saukar Alƙur’ani a matsayin abin farin ciki da alfahari.

Malam Zangon Barebari ya yi kira ga iyaye da su ƙara zage dantse wajen tallafa wa yaransu domin su riƙa zuwa makarantun Alƙur’ani, tare da yin hidima ga malamai masu karantar da su.

Ya nuna damuwa da yadda wasu iyaye ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tura yara makarantun zamani, amma su kasa ba da irin wannan kulawar ga makarantun Alƙur’ani.

Ya bayyana hakan a matsayin babban ƙalubale ga iyaye, inda ya buƙace su da babbar murya da su dage wajen tallafawa malamai masu koyar da Alƙur’ani, domin wannan ilimi shi ne zai amfani yaro a duniya da lahira.

Ya ƙara da cewa ilimin zamani ana nema ne domin duniya, wanda a ko’ina za a iya samun sa, amma ilimin Alƙur’ani sai da ƙoƙari da sadaukarwa.

Haka zalika, Malam Zangon Barebari ya yi kira ga gwamnati da ta ƙarfafa makarantun Alƙur’ani ta hanyar ba su tallafi da kulawa ta musamman, yana mai cewa zaman lafiyar al’umma ma yana da alaƙa da irin waɗannan makarantu, domin suna taimakawa wajen kwantar da fushin Ubangiji.

Ya ce idan Allah Ya yarda da al’umma, to ko hukumomi za su zauna lafiya.

A ƙarshe, ya ja hankalin ɗaliban da suka haddace Alƙur’ani da su sani cewa yanzu ne farkon tafiyarsu, ba ƙarshenta ba.

Ya ce haddace Alƙur’ani kamar samun maɓuɗin alheri ne; muddin mutum ya riƙe shi, ba zai ɓace ba, kuma zai buɗe masa ƙofofin alheri a duk inda ya dosa.

Ya ƙara da cewa idan mutum ya yi sakaci har Alƙur’ani ya subuce masa, to kamar ya yar da maɓuɗinsa ne, wanda hakan kan jefa shi cikin wahala. “Amma wanda ya kiyaye Alƙur’ani, yana da tabbacin samun sauƙi da buɗaɗɗen alheri a dukkan lamuransa, da yardar Allah,” ya ƙarƙare.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength