Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ƙungiyar ’yan kasuwar goro ta Mariri ta bayyana cewa an samu gagarumin cigaba da nasarori da dama a cikin shekaru biyu da suka gabata tun bayan karɓar shugabancin kasuwar ƙarƙashin jagorancin shugaban kasuwa, Alhaji Sabiu Bala Tsakuwa.
Sakatare Janar na ƙungiyar, Alhaji Ibrahim Sani Zara, ne ya bayyana hakan, inda ya ce an samu sauyi mai kyau a tsarin shugabanci, wanda ya samar da damar gudanar da kasuwanci cikin ’yanci da fahimtar juna, tare da kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma cigaban da ya raya kasuwar.
Ya ƙara da cewa, a halin yanzu Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da gyaran filin ajiye motoci na kasuwar, inda za a shimfiɗa kankare domin sauƙaƙa sauke goro ba tare da datti ba, tare da sanya ƙofa da kuma fitilu mai aiki da hasken rana domin ƙara inganta tsaro.
Haka kuma, ya bayyana cewa Sanatan Kano ta Arewa, Barau I. Jibrin, ya tallafa musu da fitilu masu amfani da hasken rana guda 50, waɗanda ake aikin girkawa a harabar kasuwar.
Alhaji Ibrahim Sani Zara ya yi kira ga ’yan kasuwar Mariri da su cigaba da bai wa shugabannin kasuwar goyon baya, yana mai cewa da yardar Allah kafin ƙarshen shekarar 2026, kasuwar za ta kasance cikin kasuwannin da ake alfahari da su a jihar Kano.
Haka nan ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro na kasuwar wajen tabbatar da tsaro.
A wani ɓangare kuma, ’yan kasuwar goro na Mariri sun miƙa saƙon jaje ga Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Kasuwanci, Alhaji Shehu Wada Sagagi, da Shugaban Kasuwar Singa, Barista Junaid Zakari, da sauran ’yan kasuwa bisa iftila’in gobarar da ta auku.
Alhaji Ibrahim Sani Zara ya ce an daɗe ba a fuskanci irin wannan jarabawa ta gobara ba, don haka suna addu’ar Allah Ya kiyaye gaba, Ya maye musu da alheri, tare da kawo yalwar arziƙi gare su da jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.







