Daga Ibrahim Muhammad Kano
An gudanar da taron rantsar da sabbin ɗaliban da aka ɗauka domin su yi karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasahar Lafiya ta Jameel Chiroma da ke Kano.
Taron rantsar da ɗaliban ya gudana ne a harabar Kwalejin da ke kan titin Airport, a ranar Asabar, inda ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban, iyaye da kuma malaman makarantar.
A jawabinsa bayan rantsar da ɗaliban, wanda ya assasa Kwalejin, Jamilu Abubakar Chiroma, ya ce makarantar na daga cikin makarantu biyar da suka samu rijista a ma’aikatar ilimi ta ƙasa domin gudanar da karatun Diploma na Ƙasa (ND) da kuma Babbar Diploma ta Ƙasa (HND).
Ya ce yanzu haka suna cikin tsarin JAMB Portal kamar yadda jami’o’i suke, kuma suna da shaidar sahalewa daga Ma’aikatar Lafiya ta ƙasa da kuma ta jihar Kano domin gudanar da karatu a fannin kula da lafiya.
Ya ƙara da cewa suna aiki tuƙuru domin samar da Jami’a a jihar Kano nan gaba, tare da inganta hanyoyin koyo da koyarwa.
Da yake ƙarin haske game da kafuwar Kwalejin, Jamilu Chiroma ya bayyana cewa Kwalejin ta samo asali ne daga koyar da yara darussa a unguwar Kwana Huɗu, Kaura Goje, inda aka fara da koyar da Turanci da Lissafi, daga baya aka mayar da hankali kan Lissafi kaɗai. Daga nan ne aka kafa ƙungiyar Lissafi da Kimiyya da sauran fannoni na Kimiyya har aka kai ga kafa wannan kwaleji.
Ya ce a shekarar 2022 suka samu sahalewar gudanar da Kwalejin daga Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, sannan a 2025 suka samu nasarar shiga JAMB Portal, tare da samun sahalewa daga Ma’aikatar Ilimi, lamarin da ya ba su damar fara samun ci gaba sosai.
Ya ƙara da cewa duk da cewa Kwalejin ba ta daɗe da kafuwa ba, sun riga sun yi jarabawar Council sau biyu, kuma suka samu sahalewa daga WAHEB.
Yanzu haka suna ƙoƙarin yaye ɗalibai daga shekarar 2026 zuwa 2027 a fannoni kamar Dental Surgery Technicians, Community Health, da Public Health, kuma suna shirin shiga jarabawa.
Jamilu Chiroma ya ce Kwalejin na da ɗalibai sama da 500 a fannoni daban-daban, kuma babu ɗalibin da zai kammala karatu ba tare da ya samu ƙwarewa ba.
Ya bayyana cewa suna da dakin gwaje-gwaje na Kimiyyar lafiya mai inganci, tare da kayan aiki, sannan kuɗin makarantar nasu masu sauƙi ne, har ma suna bai wa iyaye damar biyan kuɗin a hankali.
Haka kuma ya ce suna bai wa ɗalibansu tarbiyya mai kyau tare da koyarwar addinin Musulunci, suna ware maza da mata a aji, sannan suna kai ɗalibai asibitoci domin samun ƙwarewa tare da tabbatar da tsafta a koyaushe.
Jamilu Abubakar Chiroma ya ce sama da sabbin ɗalibai 200 aka rantsar a wannan karo, kuma sun fito daga sassa kamar Public Health, Health Promotion, Community Health, da Dental Health.
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka rantsar, Murtala Husaini, ya ce ya zo ne daga Rijiyar Lemo, kuma ya yaba da ƙwazon makarantar sosai.
Ya ƙara da cewa yana da ɗa guda ɗaya a Kwalejin duk da cewa yana da yara 10, kuma wannan shi ne karo na farko da ya kawo yaro makarantar.
Murtala Husaini ya ce ragowar ‘ya’yansa tara ma zai kawo su makarantar saboda gamsuwar da ya samu da irin yadda malamai ke koyarwa da kuma yadda shugaban kwalejin ke tafiyar da ita cikin tsari, tarbiyya da addini.








