Daga Ibrahim Muhammad Kano
Shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Kwalejin Nazarin Shari’a da Addinin Musulunci ta ƙasa (ACSILS), Alhaji Mahmud Garba Kabuga, ya bayyana cewa babu abin da za su ce dangane da cikar makarantar shekaru 50 da kafuwa face godiya ga Allah, domin manufofi da dalilan da aka kafa ta sun cika, har ta kai ga cewa abin da magabata suka hango ya tabbata.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen buɗe taron bikin cikar shekaru 50 da kafuwar kwalejin.
Kabuga ya ce, a da kafin samar da makarantar, har masu sauke saƙo kan zama alƙalai saboda ƙarancin ma’aikatan shari’a. Amma yanzu, a jihar Kano da ma Arewa baki ɗaya, babu inda babu ƙwararrun alƙalai saboda gudunmawar da makarantar ta bayar.
Ya ƙara da cewa makarantar ta zama tamkar uwa ga sauran irin waɗannan makarantu da aka kafa a jihohin Arewa har ma da Kudu.
Ya ce a yanzu mafi ƙarancin shaidar ilimi da ake samu a tsakanin alkalai ita ce difloma, yayin da akwai masu digiri da digirgir a fannin shari’a, yana mai cewa kusan kaso 80 cikin 100 na masu aikin alkalanci a Arewa tsofaffin ɗaliban wannan makaranta ne.
Ya ƙara da cewa tsofaffin ɗaliban AKCILS suna duban irin gudunmawar da Khadimai, alƙalai da masu muƙamin SAN da suka yi karatu a makarantar za su bayar, domin akwai buƙatar su waiwayi makarantar da ta zama asalinsu kuma ta ba su shaidar da suke amfani da ita wajen aiki.
Ya ce abin takaici ne cewa kafin zuwan ƙungiyar tsofaffin ɗaliban, makarantar ta kasance cikin halin rashin kulawa. Amma tun bayan kafa ƙungiyar sama da shekara guda da ta gabata, sun yi ayyuka da dama kamar gina ajujuwa, ɗakuna, rijiyoyin sola da gyaran wasu ajujuwa.
Haka kuma, ya yi kira ga sauran ajin-ajin tsofaffin ɗalibai da su haɗa kai su waiwayi makarantar ta ɓangaren ƙungiyarsu ta ƙasa, yana mai cewa idan suka zo da shirye-shiryensu, ƙungiyar za ta haɗa su da shugabancin makarantar domin a ci gaba da inganta ta.
Kabuga ya ce suna ci gaba da ƙoƙarin ganin Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafawa makarantar ta hanyar yin gyaran doka domin ta samu cikakken amfanin tallafin gwamnati.
Ya bayyana cewa har yanzu makarantar na fuskantar matsaloli da dama, domin mafi yawan malamai ba su da ofisoshi, sannan babu isassun kujeru a ajujuwa, yana mai cewa abubuwa sun tabarbare kafin tsofaffin ɗalibai su fara bayar da gudunmawa.
A cewarsa, da yardar Allah da taimakon hukumar makarantar da kuma ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta ƙasa, suna ƙoƙarin ganin an samu sa hannun Gwamnatin Tarayya wajen tallafawa makarantar.
Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda ta fara waiwayar makarantar, inda ta fara aikin katanga tare da gyaran wani ɗakin taro da ya ƙone, amma ya ce har yanzu akwai buƙatar ƙarin zaurukan karatu da ofisoshin malamai.








