Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Tsohon Mai Bai wa Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Shawara na Musamman kan Harkokin Addinai, Hon. Ali Baba Muhammad A. Gama Lafiya Fagge, ya ce tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya fi mayar da hankali wajen yi wa addinin Musulunci hidima fiye da harkokin siyasa.
Ali Baba ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen rufe gasar musabaƙar karatun Alƙur’ani ta ƙananan hukumomi da Gidauniyar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta shirya. An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Amani ranar Lahadi, inda ya wakilci Ganduje.
Ya ce kusan sama da shekara 25 ke nan da Gidauniyar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke gudanar da ayyukan ci gaban addinin Musulunci. A cewarsa, ayyukan gidauniyar ba su taƙaitu ga shirya gasar musabaƙar Alƙur’ani kaɗai ba, har ma da gudanar da da’awa, musuluntar da Maguzawa, ayyukan kiwon lafiya ciki har da tiyatar ido, da kuma taimaka wa wajen kula da waɗanda suka rasu sakamakon haɗurra ko wasu dalilai.
Ya ƙara da cewa gidauniyar kan samar da motar ɗaukar gawa tare da taimaka wa iyalan mamaci wajen yi masa sutura idan ba su da hali.
Ali Baba ya ce gidauniyar na kuma raba kayayyakin tallafi ga malamai da marasa galihu a watan Ramadan, baya ga gina masallatan Juma’a da makarantu a wurare daban-daban.
“Duk wani aikin da Musulunci ya yi umarni da shi domin neman lada, Ganduje yana cikinsa. Shi ya sa ma Shehin Malami Lawan Triumph ya kwatanta shi da Marigayi Sardauna, saboda yadda Sardauna ya kasance yana haɗa siyasa da hidimar addini a zamaninsa,” in ji shi.
Ya ce malamai da dama ba sa zuwa wurin Ganduje saboda neman kuɗi, sai dai saboda irin girmamawa da amincewar da suke da ita gare shi sakamakon hidimar da yake yi wa addinin Musulunci.
A cewarsa, ko lokacin da Ganduje yake Gwamnan jihar Kano na wa’adi biyu, bai bari nauyin mulki ko harkokin siyasa sun hana shi ci gaba da gudanar da ayyukan addini ba.
Hon. Ali Baba ya ƙara da cewa babu wata gwamnati da ta gudanar da aikin musuluntar da Maguzawa tare da tara malamai a gidan gwamnati kamar gwamnatin Ganduje.
“Saboda haka ya kamata mutane su yi koyi da irin waɗannan kyawawan halaye,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa Ganduje bai damu da siyasa kamar yadda yake damuwa da hidimar addini ba.
“Yanzu idan ka ce za ka ɗauki hankalinsa kan siyasa, ba za ka iya ba. Siyasa ba ita ce ta fi damunsa ba. Abin da ya fi damunsa shi ne hidimar addinin Musulunci. Kashi 90 cikin 100 na rayuwarsa yana sadaukar da shi ne ga addini, yayin da sauran kashi 10 cikin 100 suka shafi siyasa da harkokin rayuwarsa da iyalansa. Burinsa mafi girma shi ne neman lahira,” in ji shi.
Ali Baba ya kuma yi kira ga al’umma da su yi koyi da halayen Ganduje wajen tallafa wa addini da ayyukan alheri.
Ya ce, “Ba lallai sai mutum ya kasance mai arziƙi kamar Ganduje ba kafin ya yi hidima ga addini. Ko da gwangwani ne ka saya ka kai masallaci, ko ka biya wa yaran maƙwabta kuɗin makaranta, ko ka sayi Alƙur’ani ka ba da gudummawa ga masallaci, ko kuma ka halarci duk wani taron aikin alheri. Addini yana buƙatar gudummawar kowa, ko da ba da kuɗi ba ne.”








