Daga Ibrahim Muhammad Kano
Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Dakta Rabilu Muhammad, ya nada Alhaji Jamilu Lamir Jibrin a matsayin Sarkin Magani na Karamar Hukumar Fagge. Wannan sarauta ce da ya gaji bayan rasuwar mahaifinsa marigayi Dakta Lamir.
An gudanar da bikin nadin ne a fadar Sarkin Maganin dake Kano ranar Laraba, inda Sarkin ya umurci sabon Sarkin na Fagge da ya yi koyi da kyawawan halaye na mahaifinsa na kaunar al’umma, karamci, da kuma biyayya ga masarautar maganin gargajiya ta jihar Kano.
Da yake jawabi a madadin iyalan marigayi, Alhaji Mukhtar Lamir ya godewa Sarkin Maganin Kano da majalisarsa bisa wannan nadi. Ya ce: “Muna godiya sosai ga Dakta Rabilu Muhammad da ya ganu cewa dan uwamu Jamilu ya cancanci ya gaji sarautar mahaifinsa.”
A nasa jawabin, sabon Sarkin Magani na Fagge, Alhaji Jamilu Lamir Jibrin, ya bayyana jin dadinsa da farin ciki bisa wannan zabi da Allah Ya yi masa. Ya kuma godewa Allah, Sarkin Maganin Kano, da masarautar baki ɗaya.
Ya ce: “Da yardar Allah zan yi iya ƙoƙarina wajen bin sawun mahaifina na kyautatawa al’umma da ƙaunarsu. Ina kira ga matasa da su kasance masu biyayya ga iyaye da dattijai, su zauna da kowa lafiya.”
Alhaji Jamilu ya kara da cewa kamfanin hada magungunan gargajiya na LAMJIB da mahaifinsa ya kafa, da yardar Allah za su cigaba da bunkasa shi domin ya zama sananne ba kawai a Najeriya da Afirka ba, har ma a faɗin duniya.
Bikin ya samu halartar masu rike da sarautu, malamai, da jama’a masu yawa.








