Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Makarantar Khadijat Gambari Academy da ke Unguwar Yakasai a cikin birnin Kano, ta gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na 17, inda aka yaye ɗaliban da suka kammala karatu daga matakan Nursery, Primary da Sakandare.
Bikin, wanda aka gudanar ranar Asabar, ya samu halartar iyaye, malamai, ɗalibai da sauran al’ummar makarantar, inda aka gudanar da bukukuwa daban-daban domin taya ɗaliban murnar kammala karatunsu.
Da take jawabi a wajen bikin, shugabar makarantar, Hajiya Rahmatu Abdurrahman, ta ce wannan shi ne karo na 17 da makarantar ke gudanar da bikin yaye ɗalibai tun bayan kafuwarta.
Ta ce makarantar na alfahari da dimbin tsofaffin ɗalibanta da suka ci gaba da karatu a manyan makarantu, yayin da wasu daga cikinsu suka kammala karatu kuma suke aiki a wurare daban-daban.
“Alhamdulillah, muna da tsofaffin ɗalibai da yawa. Wasu yanzu haka suna jami’a, wasu kuma sun kammala karatunsu suna aiki a wurare daban-daban,” in ji ta.
Hajiya Rahmatu ta kuma nuna godiyarta ga Allah bisa kyakkyawan sakamakon jarabawar NECO da ɗaliban makarantar suka samu, tana mai cewa suna jiran sakamakon jarabawar WAEC, tare da fatan samun sakamako mai kyau.
An Karrama Iyayen Ɗalibai
Shugabar makarantar ta bayyana jin daɗinta kan kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin makarantar da iyayen ɗalibai, tana mai cewa haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu na taimakawa wajen samun nasarar karatun yara.
Ta ce saboda wannan dalili ne makarantar ta karrama wasu daga cikin iyayen ɗalibai da suka nuna ƙoƙari da kulawa ta musamman wajen bibiyar karatun ’ya’yansu.
Hajiya Rahmatu ta bayyana cewa makarantun masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa gwamnati wajen samar da ilimi ga al’umma, musamman a Jihar Kano.
Ta ce ita kanta ta daɗe tana aiki a makarantu masu zaman kansu, inda a shekarun baya take tafiya daga Yakasai zuwa Ashton Road da ke hanyar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
A cewarta, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka kafa makarantar a Unguwar Yakasai shi ne sauƙaƙa wa iyaye samun makaranta kusa da gidajensu, tare da taimaka wa gwamnati wajen faɗaɗa damar samun ilimi ga al’umma.
Kira Ga Iyaye Kan Tarbiyyar Yara
A ƙarshe, Hajiya Rahmatu ta yi kira ga iyaye da su ƙara sanya ido kan karatun ’ya’yansu da tarbiyyarsu, musamman a wannan zamani da amfani da intanet da kafafen sadarwar zamani ya zama ruwan dare.
Ta ce ya kamata iyaye su tabbatar da cewa ’ya’yansu ba sa shiga abubuwan da za su iya lalata tarbiyyarsu, maimakon haka su taimaka musu wajen amfani da intanet da sauran fasahohin zamani domin neman ilimi da ci gaban rayuwarsu.
Bikin ya samu halartar iyaye, malamai da ɗaliban da aka yaye, inda aka kammala shi cikin yanayi na farin ciki da murna.








