Shugaban Kwalejin CCEK Ya Yaba Wa Shekarau Kan Tallafin Karatu Ga Ɗalibai 850

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Community College of Education Kano (CCEK), Dakta Muhammad Adam Abubakar, ya yaba wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Sanata, Ibrahim Shekarau, bisa tallafin karatu da ya bai wa ɗalibai 850 a lokacin kafuwar kwalejin.

Dakta Muhammad ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye ɗaliban CCEK da aka gudanar ranar Asabar.

Ya ce Kwalejin ta samo asali ne daga Dala Institute of Continuous Education, wanda aka kafa a shekarar 2018 tare da hadin gwiwar National Teachers Institute (NTI), kafin daga bisani a kafa Community College of Education Kano (CCEK) a shekarar 2025.

A cewarsa, a lokacin da aka kafa Dala Institute, Sanata Ibrahim Shekarau ya nuna kishinsa ga harkar ilimi, inda ya ɗauki nauyin karatun kusan ɗalibai 850, ’ya’yan Jihar Kano, har suka kammala karatunsu.

Ya ce wannan babban tarihi ne da ba za a manta da shi ba, saboda irin gudunmawar da tsohon gwamnan ya bayar wajen bunkasa ilimi a jihar.

Dakta Muhammad ya bayyana cewa daga cikin ɗaliban da suka samu tallafin, 725 ne suka yi nasarar kammala karatunsu, kuma aka yaye su, yayin da ɗalibai 15 ke da carry-over da za su sake wasu darussa.

Yadda Ake Gudanar Da Karatu

Provost ɗin ya ce ana gudanar da karatu a Kwalejin ne tsawon kwanaki uku a mako, wato Juma’a, Asabar da Lahadi.

Ya bayyana cewa shirin karatun na neman samun shaidar NCE ne, wanda ake ɗaukar tsawon shekaru huɗu.

A cewarsa, ana karɓar ɗaliban da suka kammala sakandare tare da samun maki na credit guda huɗu, ciki har da Turanci da Lissafi.

Ya ce ana tura ɗalibai zuwa Teaching Practice a shekara ta biyu da ta uku, yayin da a shekara ta huɗu suke gudanar da aikin bincike (Project).

Ya ƙara da cewa shaidar da ɗaliban suke samu ita ce NCE, wadda National Teachers Institute (NTI) ke bayarwa.

Dakta Muhammad ya bayyana farin cikinsa kan halartar bikin da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Malam Murtala Sule Garo, da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, suka yi.

A ƙarshe, Provost ɗin ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta yi la’akari da bukatar samar wa kwalejin matsuguni na dindindin, domin hakan zai taimaka wajen kara bunkasa harkar ilimi da faɗaɗa ayyukan kwalejin.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo