Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan Yaɗa Labarai, Malam Abdul’azeez Abdul’azeez, ya yaba wa malamai da masu gudanar da Madarasatu Raudatun Nabiyyi Litahfizil Qur’an Waddirasatil Islamiyya Fagge, Kano bisa ƙoƙarinsu wajen koyar da yara ilimin addini da Al-Qur’ani tare da ba su tarbiyya mai kyau.
Abdul’azeez ya bayyana hakan ne a yayin bikin saukar Alƙur’ani karo na farko da kuma taron karrama wasu daga cikin mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimi da makarantar.
Ya ce irin waɗannan makarantu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ilimi da kyakkyawar tarbiyya a tsakanin al’umma.
Saboda haka, ya yi kira ga iyaye da sauran al’umma da su ci gaba da tallafa wa makarantu irin wannan, domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A yayin taron, Abdul’azeez ya kuma sanar da bayar da gudunmawar Naira 250,000 domin tallafa wa makarantar da kuma ƙarfafa ayyukan ilimi da take gudanarwa.
Da yake jawabi, Shugaban Makarantar, Malam Magaji Ibrahim Abdullahi, ya ce bikin shi ne karo na farko da makarantar ta gudanar tun bayan kafuwarta a shekarar 1435 bayan hijira, wadda ta yi daidai da shekarar 2013.
Ya ce makarantar ta fara ne da ɗalibi guda a cikin gida, kafin daga bisani ta bunƙasa tare da koma wa tsarin makaranta.
Ya ƙara da cewa a lokacin zaman gida da aka yi sakamakon annobar Korona, adadin ɗaliban makarantar ya ƙaru sosai, inda suka kai kusan 1,000.
A halin yanzu, ya ce makarantar tana da ɗimbin ɗalibai da malamai da ke gudanar da koyarwa a fannoni daban-daban na ilimin addini da Alƙur’ani.
Malam Magaji ya bayyana cewa ɗalibai 40 ne suka kammala haddar Alƙur’ani a wannan karon, inda 25 daga cikinsu maza ne, yayin da 15 mata ne.
Ya ce ɗaliban makarantar suna samun cikakken haɗin kai daga iyayensu, duk da cewa makarantar na fuskantar wasu ƙananan ƙalubale.
Shugaban makarantar ya kuma bayyana cewa kusan mutane 70 ne aka karrama a wajen taron saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban makarantar da harkar ilimi.
Ya ce waɗanda aka karrama sun haɗa da waɗanda suke raye da kuma waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, ciki har da malamai, ’yan siyasa, limamai, ladanan masallatai da sauran jiga-jigan al’umma.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Farfesa Umar Sani Fagge, Alhaji Hamisu Ɗanwawu, Alhaji Sagir Abba, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, da sauran masu ruwa da tsaki daga Ƙaramar Hukumar Fagge.








