Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ƙungiyar makarantun Sakandaren Kimiyya ta jihar Kano, wadda aka fi sani da KASSOSA, ta karrama fitaccen Malamin Lissafi, marigayi Malam Haruna Ungogo, bisa irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi.
An yi wannan karramawa ne a yayin taron shekara-shekara da ƙungiyar ta gudanar.
Dakta Sulaiman Muhammad, shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Dawakin Tofa (aji na 1984), shi ne ya karɓi takardar karramawar a madadin marigayi Malam Haruna Ungogo.
A jawabinsa, Dakta Sulaiman Muhammad ya bayyana cewa karramawar ta nuna hangen nesa da kyakkyawan tunani na ƙungiyar KASSOSA, kasancewar marigayi Malam Haruna Ungogo malami ne nagari, jajirtacce kuma mai sadaukarwa, wanda ya bayar da gagarumar gudummawa da ta taimaka wa ɗalibai da dama har suka kai matsayin da suke a yau.
Ya ƙara da cewa, duk da irin rawar da iyayensu suka taka wajen tura su makaranta, gudummawar da Malam Haruna Ungogo ya bayar ta zarce misali.
A cewarsa, samun malamai masu kishin ɗalibai irin nasa abu ne mai wahala a wannan zamani.
Dakta Sulaiman ya bayyana cewa a lokacin da suke karatu, marigayin yana aiki ne da tsoron Allah, inda sau da dama yake shiga aji ya koyar, ko da ba lokacinsa ba ne, musamman idan ya lura babu malami.
Ya ce koyaushe yana shirye ya taimaka wa ɗalibai da ma ma’aikata ba tare da gajiya ba.
A ƙarshe, Dakta Sulaiman Muhammad ya gode wa ƙungiyar ƙasa ta KASSOSA bisa wannan karramawa, tare da yaba wa gwamnatoci daban-daban da suka taimaka wajen kafa makarantun Sakandaren Kimiyya.
Ya kuma yi kira da a ƙara ba wa makarantun goyon baya domin su tsaya da ƙafarsu tare da ci gaba da cika manufar da aka kafa su a kai.








