Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Buhunan Takin Zamani 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon buhunan taki 72,000 kyauta tare da magungunan kashe ciyawa da sauran kayan aikin noma ga manoma a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce na ƙara bunƙasa harkar noma da tabbatar da wadatar abinci.

An ƙaddamar da shirin rabon takin daminar shekarar 2026 ne a ranar Juma’a a Trade Fair Complex da ke Gusau, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta raba buhunan taki 72,000, lita 200,000 na magungunan kashe ciyawa, da kuma injuna 100 na sarrafa ragowar amfanin gona.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an kuma samar da injuna 100 na yankan ciyawar kiwo, injuna 100 na niƙa abincin dabbobi, iri na ingantacciyar ciyawar kiwo, babura 20 da wayoyin hannu 20 domin jami’an ba da shawara kan harkokin noma.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya ce Zamfara na daga cikin jihohin da ke da muhimmiyar rawa a fannin noma a Niueriya saboda yalwar ƙasar noma da kuma ƙwazon al’ummarta.

Ya ce, rabon kayan aikin noman wani sabon mataki ne na cika alƙawarin gwamnatinsa na farfaɗo da harkar noma, ƙarfafa wadatar abinci, samar da hanyoyin dogaro da kai ga al’umma da kuma mayar da Zamfara ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin noma a ƙasar.

A cewarsa, noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jihar, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci, yaƙi da ayyukan ‘yan bindiga da sauran laifuffuka.

“Noma ba kawai hanyar samun kuɗi ba ce, yana cikin tarihinmu da al’adunmu, kuma shi ne tubalin da za a gina cigaban da al’ummarmu za su ci gaba da amfana da shi a nan gaba,” inji gwamnan.

Lawal ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shi ne sauya noma daga tsarin dogaro da kai zuwa noma na zamani da ke amfani da fasaha tare da mayar da hankali kan kasuwanci.

Ya ce hakan za a cimma ne ta hanyar samar da ingantaccen taki da iri, amfani da injinan noma, bunƙasa ban ruwa, ƙarfafa ayyukan jami’an wayar da kan manoma, amfani da dabarun noma masu dacewa da sauyin yanayi da kuma samar da kasuwannin sayar da amfanin gona.

Gwamnan ya ce da dawowar zaman lafiya a wasu yankunan jihar, ƙarin al’ummomi na komawa gonakinsu, yayin da iyalai ke sake farfaɗo da hanyoyin samun abin dogaro.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta nuna jajircewarta ba ta baki kaɗai ba, har ma ta hanyar haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, abokan hulɗar ci gaba da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, tare da biyan kuɗaɗen da suka rataya a wuyanta domin tabbatar da jihar ta ci gajiyar shirye-shiryen bunƙasa noma.

A cewarsa, shirye-shirye irin su FADAMA III, NG-CARES, SPIN, ZACADEP, SAPZ, da shirye-shiryen da Asusun IFAD ke tallafawa sun taimaka wa dubban manoma da ingantattun iri, taki, magungunan noma, kayan ban ruwa, kayan aikin gona da kuma ilimin noma na zamani.

Ya ce waɗannan tsare-tsare na ƙara yawan amfanin gona, faɗaɗa gonaki da bunƙasa kuɗaɗen shiga na gidaje, tare da gina tubalin samar da ingantaccen tsarin noma mai jure sauyin yanayi.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa rabon takin da sauran kayan aikin noman zai shafi dukkan mazabu 147 na siyasa da ke ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A ƙarƙashin tsarin rabon, kowace mazaba za ta karɓi buhunan taki 340, yayin da kowace ƙaramar hukuma za ta samu lita 8,000 na magungunan kashe ciyawa.

Related Posts

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum