NDC Ta Nuna Damuwa Kan Harin Da Aka Kai Wa ‘Yan Jarida A Taron APC Na Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) reshen Jihar Kano ta nuna matuƙar damuwa tare da yin Allah wadai da farmakin da aka kai wa wasu ‘yan jarida a yayin taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Kano a kwanakin baya.

Shugaban NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isa Mairiga, ne ya bayyana hakan a madadin jam’iyyar da kuma jagoran Kwankwasiyya na ƙasa kuma jagoran NDC na Arewa, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.

Mairiga ya ce jam’iyyar NDC da jagoranta suna miƙa saƙon jaje ga ‘yan jaridar da abin ya shafa, tare da yin Allah wadai da lamarin da kuma addu’ar Allah Ya kiyaye afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Ya ce irin wannan hali ba ya cikin tsarin NDC, yana mai cewa jam’iyyar ba ta goyon bayan cin zarafin ‘yan jarida ko ma abokan hamayya.

“Ba mu da wannan ɗabi’a, ba ma ‘yan jarida kaɗai ba, ko ma abokin hamayya. Me kake so ɗan jarida ya yi maka? Shi ne yake wahala yana tallata ka da ayyukanka. Idan ka ce za ka farmaki ɗan jarida ko ka wulakanta shi, wa kake so ya yaɗa maka abin da kake son yi?” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jagoran Kwankwasiyya na ƙasa, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, bai koya musu irin wannan ɗabi’a ba, yana mai tabbatar da cewa NDC za ta ci gaba da kare mutuncin ‘yan jarida da na sauran ‘yan ƙasa.

Husaini Isa Mairiga ya kuma ce idan aka samu damar jagorantar al’umma a ƙarƙashin NDC, za su yi ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da inganta tsaro, tare da samar da yanayin da kowa zai iya gudanar da harkokinsa cikin kwanciyar hankali.

Ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa a faɗin jihar da su ji tsoron Allah, su guji cin mutuncin mutane, farmaki da lalata dukiyoyi ba bisa ƙa’ida ba domin biyan buƙatun siyasa, yana mai cewa amfani da ‘ya’yan mutane wajen aikata irin waɗannan abubuwa ba abu ne da ya dace ba.

  • Related Posts

    INEC Ta Tabbatar Da Nafiu Sankara A Matsayin Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sunan Dakta Nafiu Sankara a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar PDP…

    An Rantsar da Sabbin Shugabannin ANCOPSS a Kano da Raba Magunguna Ga Makarantun Kwana 20

    Daga Ibrahim Muhammad Kano An rantsar da sabbin shugabannin Kungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, ANCOPSS, tare da raba magunguna ga makarantun kwana na jihar Kano. A yayin taron,…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano