Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Kwalejin Amina Comprehensive, da ke Tudun Rubudi a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, ta gudanar da gagarumin bikin saukar Alƙur’ani ga ɗalibanta 15.
An gudanar da bikin ne a ɗakin taro na Mumbayya da ke Gwammaja, inda iyayen yara, shugabannin al’umma, malaman addini, ‘yan kasuwa da sauran baƙi suka halarta.
Da yake jawabi a wajen taron, Daraktan makarantar, Malam Sunusi Ibrahim Kulita, ya ce an shirya bikin ne domin taya ɗaliban da suka kammala haddar Alƙur’ani murna, tare da karrama mutum 10 da suka ba da gudunmawa wajen bunƙasa ilimi da addini.
Ya ce daga cikin waɗanda aka karrama akwai Hajiya Amina Musa, Hajiya Goggo Fatima Dantata da tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gwale, Hon. Muhammad Kasim Warure.
Malam Sunusi ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da makarantar ta gudanar da bikin saukar Alƙur’ani tun bayan kafuwarta.
A cewarsa, makarantar ta fara ne da ɗalibai uku kacal cikin gwagwarmaya da dogaro ga Allah, amma a halin yanzu tana da ɗalibai sama da 150 da malamai bakwai, maza da mata.
Ya ƙara da cewa makarantar ta gina ajujuwa bakwai a filinta, inda aka kammala biyu kuma ake ci gaba da gudanar da karatu a cikinsu, yayin da ake ci gaba da neman taimakon Allah domin faɗaɗa ayyukan makarantar.
Bikin ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da malaman addini, shugabannin al’umma, masu riƙe da sarautun gargajiya, ‘yan kasuwa, iyayen yara, malamai da sauran ɗalibai.







