Yin Amfani Da Lokaci Wajen Neman Ilimi Na Da Matuƙar Muhimmanci -Hon. Muhammad Ƙasim Warure

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwale, Hon. Muhammad Kasim Warure, ya jaddada muhimmancin amfani da lokaci wajen neman ilimi, yana mai cewa ilimi shi ne ginshiƙin rayuwa.

Warure ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen bikin saukar Alƙur’ani na ɗalibai 15 da Makarantar Amina Comprehensive College ta shirya a ɗakin taro na Mumbayya da ke Gwammaja, inda kuma aka karrama shi saboda gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da addini.

Ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa wannan karramawa, yana mai cewa ko gayyatar da aka yi masa halartar taron ita kaɗai babbar girmamawa ce.

“Ba abin da za mu ce wa Allah sai godiya. Idan aka zo batun ilimi kuwa, shi ne gishirin rayuwa. Wani lokaci idan mutum ya manyanta, duk irin ilimin da ya samu sai ya ji da a ce tun farko ya ƙara dagewa wajen neman ilimi,” in ji shi.

Hon. Warure ya yi kira ga matasa da ɗalibai da su yi amfani da lokacinsu yadda ya kamata wajen neman ilimi, yana mai cewa lokaci idan ya wuce ba ya dawowa.

“Duk wanda Allah ya ba damar neman ilimi ya kamata ya ƙara jajircewa, domin lokaci yana tafiya ne kuma ba za a sake samun irinsa ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tun suna ƙanana suka taso suna ganin iyayensu da kakanninsu suna hidimtawa Alƙur’ani mai girma, abin da ya sa suke ba da muhimmanci ga duk wani aiki da ya shafi addini.

“A duk inda aka gudanar da wani aiki na hidimtawa Alƙur’ani, bai kamata mutum ya jira sai an gayyace shi ba. Duk inda za ka iya ba da gudummawa, ya dace ka kasance a gaba,” in ji shi.

Hon. Muhammad Kasim Warure ya kuma yaba wa shugabannin Makarantar Amina Comprehensive College bisa ƙoƙarin da suke yi wajen tarbiyyantar da yara a fannin ilimin addini da na zamani, tare da addu’ar Allah Ya ƙara musu ƙarfin guiwar ci gaba da wannan aiki na alheri.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo