Makarantar AL-AZHAR Tana Ƙarfafa Ɗalibanta Zama Masu Amana Da Ikhlasi

Daga Ibrahim Muhammad

Makarantar Al-Azaha a jihar Kano ta gudanar da taron bukin yaye ɗalibai da raba kyautuka ga ɗalibai masu ƙwazo a harabar makarantar ranar Asabar da ya sami halartar ɗimbin iyaye da sauran manyan baƙi.

Da suke ƙarin bayani game da taron, Daraktocin makarantar su biyu. Furofesa Binta Tijjani Jibrin da Furofesa A’ishatu Abdu Isma’il da sune suka kafa makarantar sun bayyana irin ɗimbin gudunmuwa da makarantar ke bayarwa ga bunƙasa cigaban ilimi.

A bayanin ta Furofesa A’ishatu Abdu Isma’il ɗaya daga daraktocin makarantar ta bayyana cewa taron ana shirya shi ne kowace ƙarshen shekara, saboda bai wa sauran yara ƙarfin gwiwa, su a makarantar Al-Azhar abin da suka fi ƙarfafawa shi ne koyawa yara zama masu amana da iklasi shi ya sa suke koyawa yara karatu sosai da tarbiyya ta addinin Musulunci.

Ta ƙara da cewa suna ƙoƙarin cusa tarbiyya ta hanyar ɗora ɗalibai a kai tsayawa a kan shi ya sa ma ba su yarda da satar amsar jarabawa ba a makarantar duk abin da aka gani na ƙwazon ɗalibai haka yake haka aka koya musu, kuma ana samun nasara.

Tun daga kafa makarantar suna bibiyar ɗalibansu da kyau wanda suka je jami’o’i da manyan makarantu sukan samu ɗalibai daga Al-Azhar na zama masu ƙwazo a ajinsu.

Ta ce ana samu ɗaliban da suka fito daga makarantar su suna gama jami’a ko babbar makaranta da sakamako mai kyau da yawancin su wasu sun zama likitoci, lauyoyi, injiniyoyi da manyan ma’aikata a wurare da yawa, kuma ana samun su da ƙwazo da tarbiyya da riƙon amana.

Ita ma ɗaya daga cikin daraktan makarantar ta Al-Azhar, Furofesa Binta Tijjani Jibrin ta ce in ana maganar tarbiyya, mutunci da riƙon amana ana samun sane ta tushen koyarwar addinin Musulunci shi ne ginshiƙi, don haka ilimi na zamani mai muhimmanci ne shi ya sa da suke gyara inda suka ya gurɓace su cire duk wani abu da zai ɓata tarbiyya. Sannan su koyawa ɗalibansu wannan tasa shi suke haɗa ilimin addini da na zamani a makarantar.

Ta ce tun kafa makarantar a 2000 sun ɗauki ilmi da bayar da tarbiyya a matsayin haƙƙi ne na iyayen yara da makaranta da ake haɗa hannu don tabbatar da shi suna da hanyoyi da yawa da suke shigo da iyaye harkokin makarantar domin su taya su wannan aiki suna kuma samun goyon bayan iyayen yara kashi 90 bisa 100.

Furofesa Binta Tijjani Jibrin ta ce suna da tsare- tsare na tallafa wa ‘ya’yan malamai da na ma’aikatan makarantar da ‘ya’yan al’umma da suke kewaye da makarantar suna kuma da tallafawa wasu makarantun gwamnati da suke kusa da su ta hanyar horar da malamansu da tallafi ga makarantun da bai wa yara masu ƙwazo tallafin kuɗin makaranta scholarship.

Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida shugaban kwamitin iyaye da malamai na makarantar Al-Azhar, Alhaji Ibrahim Danyaro shugaban Dattawan kasuwannin Sabon Gari da Singa ya ce suna farin ciki da taron yaye ɗaliban domin rana ce da makarantar ke nuna ta kai matsayin da ya kamata a wajen bayar da tarbiyya da ba da ilimi guda biyu.

Ya ce makarantar da farko ta yi suna ne wajen ba da ilimin zamani, amma yanzu tana ƙoƙarin juyawa wajen bayar da ilimin addinin Musulunci, wanda da ma shi ne abin da ya kamata a samu ‘ya’yan Musulmi a kai su zama ‘yan boko kuma masana a kan addinin ta wannan za a ci riba biyu an haɗa ilimi biyu da zai amfanar da al’umma.

Ya yi nuni da cewa makarantar Al-Azhar na ƙoƙarin ta sauke nauyin wajen ‘ya’yan Musulmi maza da mata, kuma irin wannan makarantu suna taimakon gwamnati ne, domin idan aka ce makarantun gwamnati sune za a dogara da su ilimi ne zai faɗi domin kowa ya san makarantun gwamnati ba sa iya sauke nauyi na al’umma.

Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya ce dole ne mutane su riƙa kawo wa gwamnati tallafi su ba da kawo gudummawa yadda za a haɓaka ilimi, domin idan ba don makarantu masu zaman kansu suna ba da gudunmawa ba, ba za a samu haɓakar ilimi yadda ya kamata ba.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength