Daga Ibrahim Muhammad
Ganin irin cigaba da duniya take samu a harkar Kimiyya da Fasaha tasa kwamitin cigaban mazaɓa a ƙaramar hukumar Nasarawa suka bijiro da tsarin ba da horo ga al’ummarsu a matakin sanin ilimin Kimiyya musamman ilimi na ɓangaren harkar kula da lafiya da kuma sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa ta samar da cibiya ta horar da matasa da aka sa wa suna Ibrahim Khalil Standard Academy.
Alhaji Muhammad Nuruddeen Lawan Magajin Garin Gwagwarwa, shugaban Kwamitin cigaban mazaɓa (WDC) a ƙaramar hukumar Nasarawa da ke zantawa da ‘yan jarida ya ce an buɗe cibiyayi da suka kai 18 a jihar Kano da sunan shehun Malami Ibrahim Khalil ne saboda fice da karɓuwa da ya yi da irin ƙoƙarinsa da ƙwazo kuma duk abin da aka jingina shi da shi al’umma da gwamnati za su gamsu da shi.
Ya yi nuni da sun soma da koyar da ilimi da na’ura mai ƙwaƙwalwa saboda ne saboda sha’awar yara a Kano su karɓi ilimin su shiga a dama da su, cigaba da ake samu ya zama mun amfana da shi a jihar Kano.
Ya ƙara da cewa idan aka tara ɗaliibai musamman ma mata ka tambayi mene ne burin su a rayuwa kashi 80 cikin 100 za su ce so suke su zama Likita ko ma’aikaciyar jinya ko aikin asibiti.
Wannan buri ne na akasarin ɗalibai mata. A jihar Kano sai suka ga ana da buƙatar likitoci, malaman asibiti da ma’aikatan jinya idan aka yi la’akari da ɗimbin al’umma da take da su sama da miliyan 20.
Ya ce samar da malaman lafiya da za su kula da mutane M20 a bar wa gwamnati ita kaɗai ba zai yiwu ba, wajibi ne jama’a su shigo don tallafawa ‘ya’yan al’umma wajen karatu, musamman na Kimiyya.
Wannan ya ba su dama suka buɗe ajujuwan Kimiyya suna ɗebo yara ‘yan ajin babbar Sakandire tun daga 1,2,3 suke ba su horo na karatu a kan ilimin Lissafi da Turanci da darussan Kimiyya, idan suka ba su ilimi mataki -mataki aƙalla akwai matakai uku wanda idan Allah ya yarda yaro ya zauna ya yi karatun bisa ƙa’ida da aka yi shi suna sa ran za su iya tsallake jarabawar da za ta ba su dama su kai ga samun karatun lafiya suna da tabbacin in yaro ya yi JAMB zai ci, idan ya nemi shiga makarantar jinya ko unguwar zoma ko karatun Likita ko makamantan irin waɗannan makarantu zai iya samun nasara a ɗauke shi ya yi karatun.
Muhammad Nuruddeen ya ce sun gwada a mataki na ɗaya na biyu na uku yaran sun kai gaci da yawansu kuma suna manyan makarantu suna karatu sukan yi amfani da wannan dama su je da kansu manyan makarantu da suke koyar da harkar lafiya su nemawa wanda suka sami horo gurbin karatun, kuma bisa wannan shimfiɗe ne da suka ɗauki suke ba su gurbin karatu, kuma su yi karatun a yi nasara.
Ya ce yanzu a jami’o’i da makarantun lafiya suna da ɗalibai da suka sami wannan horon suka ci jarabawar JAMB da yawa suna karatu kuma a tsarin tafiyar da ake kusan duk waɗanda suke taimakawa wajen koyarwa a cibiyar malamai ne gogaggu masana da suke sadaukar da lokutan su suna bai wa ‘ya’ya da kanne gudunmuwa don a cimma nasara.
Ya ce sakamakon irin nasara da ake samu sai suka haɗa kai a dukkan cibiyoyin jihar Kano suka nemi gwamnatin jihar Kano ta sahale irin waɗannan cibiyoyi a dafa musu, su taso su ma su kai gaci da za su zama makarantu na al’umma masu zaman kansu a jihar Kano, kuma abin jin daɗi gwamnatin jihar Kano da ɓangaren hukumar lafiya an yi zama da su a lokuta da dama an ba da shawarwari da ƙa’idodi da sharaɗai da za ta cika su gwamnati za ta dafa mata ta zama cikin makarantu da za ta riƙa ba da horo.
Magajin Garin Gwagwarwa, Alhaji Muhammad Nuruddeen ya ce su ma sun sami sahalewa ta samar da Kamawa College of Health Science Technology, gwamnati ta yi musu rijista ta ba su ƙa’idodi da aka shimfiɗa, kuma yanzu haka sun cika kusan kashi 85 sun samar da cibiya babba a garin Ɗambatta da a nan aka kafa Kwalejin Lafiyar da Fasaha na Kanawa an samar da wuri da kayan aiki da ajujuwa na makarantar a Ɗambatta.








