MUHAMMAD ISKEEL YA ZAMA SABON MANAJA TOZALI TV

Gidan talabijin na Tozali ya sanar da naɗa fitaccen ɗan jarida da ke zaune a Kaduna, Muhammad Iskeel Abdullahi a matsayin sabon Manaja.

A wata sanarwa da tashar ta fitar yau Litinin, ta bayyana cewa, wannan matakin da suka ɗauka na nufin ƙara ƙarfafa matsayin tashar a matsayin babbar murya a kafafen yaɗa labarai na Nijeriya.

Muhammad Iskeel, wanda yana ƙwarewa a harkar yaɗa labarai, sadarwa da ƙirƙira, ya kwashe fiye da shekaru 20 yana taka rawa a fanni.

“Mun yi farin ciki da maraba da zuwan Iskeel gidan Tozali TV,” in ji Maimuna Yaya Abubakar, Shugabar Tozali TV.

Ya bayyana cewa sun yi imani Muhammad Iskeel zai yi amfani da kwarewar da gogewarsa, basirar dabarunsa, da kuma sha’awar bayar da yake da ita wajen kawo cigaba a tashar Tozali TV .

Kafin zuwan Iskeel Tozali TV ya yi wasu ayyuka daban-daban na jagoranci, ciki har da Janar Manaja na Vision FM Katsina, babban Manajan Liberty TV/Radio Kano, da Janar Manaja, Labarai da Al’amuran yau da kullum a Babban Ofishin Liberty TV da ke Abuja.

A lokacin da yake amsar aikin da aka ba shi, Muhammad Iskeel Abdullahi ya bayyana cewa, “Ina farin ciki da shiga Tozali TV, tare da alwashin ba da gudummawa ƙwarewata don ci gaba da samun nasarar tashar.”

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum