A ranar Talata, 9 ga Satumba, 2025 ne kamfanin Opay Digital Services Limited da ke hada-hadar cire kuɗi, ya ƙaddamar da wani gagarumin shiri na ba da tallafin karatu na Naira miliyan 60 ga ɗaliban Jami’ar Bayero, Kan da nufin ƙarfafa ilimi.
A wajen wani ƙwarya-ƙwaryar taron da aka shirya, an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, wanda Farfesa Haruna Musa ya wakilci Jami’ar ya sa hannu a madadinta.

An samu nasarar bayar da tallafin ne ta hanyar ƙoƙarin ƙungiyar ɗalibai (SUG) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Abdullahi Usman Baba, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS).








